in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Koroma ya jinjinawa Sin game da gudummawarta ga yaki da cutar Ebola
2014-12-03 10:11:49 cri

Shugaba Ernest Bai Koroma na kasar Saliyo, ya jinjinawa kasar Sin game da tallafin da take baiwa aikin yaki da cutar Ebola a sassan yammacin Afirka, ciki hadda kasarsa.

Shugaba Koroma ya bayyana hakan ne, yayin ganawarsa da babban wakilin kasar Sin mai kula da ayyukan yaki da cutar Ebola Xu Shuqiang, wanda ya ziyarce shi a fadar gwamnatin kasar a jiya Talata.

Ya ce, matakan da kasar Sin ke dauka a wannan fanni na nuna aniyarta ta ci gaba da kasancewa kawa ta musamman ga kasar Saliyo.

Shugaban na Saliyo ya bayyana samar da kayayyakin aiki, da kudade, da kafa dakunan bincike, a matsayin matakan da Sin ta dauka da suka dace da bukatar da ake da ita a wannan gaba.

A daya bangaren kuma shugaba Koroma ya ce, horas da jami'an lafiya 4,000 da Sin ta dauki nauyi zai taimaka matuka, tare da karfafa sashen lafiyar kasar a bangaren yaki da Ebola, dama sauran cututtukan dake addabar al'umma.

Daga nan sai ya yi maraba da shirin kafa cibiyar bincike kan cututtuka masu yaduwa a kasar, wadda za ta samar da damar horas da jami'an kiwon lafiya. Wadanda za su ci gaba da jibintar bukatun al'ummar kasar a fannin lafiya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China