Shugaban Guinee ya nuna yabo da tallafin gwamnatin kasar Sin wajen yaki da cutar Ebola
Shugaban kasar Guinee Alpha Conde ya bayyana jin dadinsa da nuna yabo a ranar Jumma'a ga gwamnatin kasar Sin game da tallafin da take baiwa kasar Guinee wajen yaki da cutar Ebola. Tun farkon barkewar wannan annobar, kasar Sin ta tsaya a koda yaushe kusa da kasar Guinee kuma ta sanya hannu wajen bada taimako, musammun ma tare da manyan jiragen saman shake da magunguna, da taimakon kudi, in ji shugaba Conde a yayin wata ganawa tare da kwamishinan gwamnatin kasar Sin dake kula da yaki da cutar Ebola a nahiyar Afrika, mista Xu Shuqiang, da ya isa birnin Conakry a ranar Jumma'a. Muna fatan cewa gwamnatin kasar Sin, dake ci gaba da ba mu tallafi, za ta ci gaba da rakiyarmu kan bukatunmu na gaba, in ji shugaban kasar Guinee. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku