Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta kaddamar a ranar Laraba a birnin Lagos, cibiyar tattalin arzikin Najeriya, da wani kamfen ta hanyar sakon SMS mai sunan "Afrika na yaki da Ebola" da ya shafi tattara kudade domin yaki da wannan cuta. Bikin kaddamar da wannan kamfen ta hanyar sakon SMS ya zo lokaci guda da tunawa da ranar da Najeriya ta tura ma'aikatan lafiya 250 zuwa kasashen dake fama da cutar Ebola, bisa tsarin tawagar kungiyar AU na tallafawa yaki da annobar Ebola a yammacin Afrika. Kamfanonin sadarwa dake nahiyar Afrika wadanda suka hada da Airtel, Econest Wireless, Etisalat, Millicom (Tigo), MTN Group, Orange, Safaricom, Vodacom da Vodafone Ghana sun shiga wannan kamfen.
Da take jawabi albarkacin bikin kaddamarwa, shugabar kungiyar AU, Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana jin dadinta kan wannan tallafi dake fitowa daga yankunan Afrika daban daban domin yaki da annobar cutar Ebola a yammacin Afrika. Haka kuma, babbar jami'ar AU, ta nuna yabo kan taimakon da shugabannin tattalin arzikin Afrika suka bayar wajen yaki da Ebola, da ma yaki da sauran cututtuka makamantan haka, tare da amincewa da gudunmuwarsu kan wannan aikin. (Maman Ada)