Shafin yanar gizo na hukumar ta FAO, ya bayyana cewa kowace kasa daga kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo za ta samu kudi har dala dubu 500, kadaden da za a yi amfani da su wajen goyon bayan sabon shirin tinkarar matsaloli a yankunan da FAO ta gabatar, matakin da zai amfani jama'a kimanin dubu 45.
An ce shirin zai kunshi horar da kwararru, da zuba jari ga aikin gona, da taimakawa iyalan manoma wajen inganta rayuwarsu, da samun kudin shiga.
Kaza lika an hakaito maganar babban diraktan kungiyar FAO Jose Graziano Dasilva, wanda ya ce tallafin kudin ya yi daidai da burin kasashen Afirka, na taimakawa juna da cimma moriyar juna. (Zainab)