A yau ne a nan birnin Beijing shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya halarci taron dandalin tattaunawa a tsakanin kasashen Afirka ta Kudu da Sin ta fuskar kasuwanci da cinikayya tare da bayar da wani jawabi.
A cikin jawabinsa, shugaba Zuma ya ce, kasarsa na sa ran raya tattalin arzikinta bisa hadin gwiwar da ke tsakaninta da Sin. Zuma ya kuma yi fatan kasashen 2 za su inganta hada kan da ke tsakaninsu a fannonin cinikayya, makamashin nukiliya, yawon shakatawa, harkokin kiwon lafiya, albarkatun teku, fasahar tauraron dan Adam da dai sauransu. (Tasallah)