in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugabar majalisar dattijai ta Rasha
2014-09-23 20:54:20 cri

Yau Talata 23 ga wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da Valentina Matviyenko, shugabar majalisar dattijai ta Rasha a nan Beijing.

A yayin ganawar, mista Li ya ce, kasar Sin na son habaka hadin gwiwa da kasar Rasha a fannonin tattalin arziki, cinikayya, zuba jari, makamashi, fasahar zamani, al'adu da dai sauransu. Kasar Sin na son shiga ayyukan more rayuwar jama'a da Rasha za ta gudanar kamar hanyar dogo mai saurin tafiya, kyautata hanyoyin dogo, a kokarin samun moriyar juna da nasara tare.

A nata bangaren kuma, madam Matviyenko tana maraba da firaministan kasar Sin da ya ziyarci Rasha cikin sauri. Bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin na samar da sabuwar dama wajen yin hadin gwiwa a tsakanin Rasha da Sin. Rasha na son inganta mu'amala da hadin gwiwa da Sin a sassa daban daban. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China