Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a yayin zaman kwamitin tsaron majalissar na jiya Juma'a, ya kara da cewa ana fatan MDD da hukumar kiwon lafiyar ta WHO, za su gaggauta ci gaba da karfafa ayyukan bincike, da kandagarkin yaduwar cutar Ebola, da kuma nazari kan bayanan da aka samu game da yaduwar cutar daga dukkan fannoni. Kana da bada jagoranci ga gamayyar kasashen duniya wajen yin hadin gwiwa tare domin samun cikakkiyar nasarar da aka sanya gaba.
Bugu da kari, Liu Jieyi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da gamayyar kasashen duniya, domin taimakawa jama'ar kasashen nahiyar Afirka da wannan annoba ta shafa.
A wani ci gaban kuma kwamitin sulhun MDD ya fidda wata sanarwa, dake bayyana damuwa dangane da mummunan tasirin da cutar Ebola ta haifar ga kasashen yammacin Afirka. Sanarwar ta kuma yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su gaggauta taimakawa, domin kasashen da abin ya shafa su iya fuskantar yaki da cutar yadda ya kamata. (Maryam)