A gun bikin mika kayayyakin, jakadan kasar Sin dake kasar Togo Liu Yuxi ya yi bayani kan wadannan kayayyaki, kana ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kara tura likitoci zuwa kasar Togo don horar da likitoci da ma'aikatan yin rigakafin da cutar a kasar.
Firaministan kasar Togo kuma ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Kwesi Séléagodji Ahoomey-Zunu a jawabinsa ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin bisa ga goyon baya da taimako da take bai wa kasarsa, kana ya yi nuni cewa, kasar Sin ta kasance wani misali na nuna sahihanci kan samar da gudummawa ga kasashe masu fama da cutar Ebola. Haka zalika kuma ya bayyana cewa, kasarsa ta Togo za ta yi amfani da kayayyakin da Sin ta samar wajen ci gaba da gudanar da ayyukan rigakafi da yaki da cutar Ebola a kasar yadda ya kamata. (Zainab)