Hukumar WFP ta bayyana cewa, annobar Ebola ba matsala ce ta wata kasa kawai ba, babban kalubale ne da ya shafi kasashen duniya baki daya. Ya zuwa yanzu, gamayyar kasa da kasa ta riga ta samu ci gaba wajen biyan bukatun jama'an da suke fama da cutar. Kasar Sin ta riga sauran kasashen duniya wajen daukar matakan bayar da taimako. Daga lokacin da aka samu barkewar cutar, gwamnatin kasar Sin ta samar wa kasashen yammacin Afirka da ke fama da cutar taimakon jin kai da darajarsa ta kai kudin Sin RMB yuan miliyan 750, wannan ya alamta cewa, kasar Sin tana cika alkawarin da ta yi wa duniya wajen samar da kayayyakin jin kai, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. (Sanusi Chen)