Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce, ta na ci gaba da hadin gwiwa da mahukuntan kasar Mali, a yakin da kasar ke yi da yaduwar cutar Ebola.
A cewar kakakin MDDr Stephane Dujarric, ya zuwa yanzu mahukuntan Mali sun tabbatar da kamuwar mutane 6 da cutar, kuma tuni 5 daga cikin su suka rasu.
Kaza lika ma'aikatar lafiyar kasar ta Mali ta kara yawan jami'an dake kula da yaduwar cutar, tare da kara kaimi ga aikin tantance matafiyan dake zirga-zirga ta filin tashi da saukar jiragen saman birnin Bamako.
A daya bangaren kuma, asusun yara na UNICEF ya fadada matakan yaki da yaduwar cutar ta Ebola a kasar, ta hanyar kara yawan kayayyakin bukatun kiwon lafiya, ciki hadda tsaftacaccen ruwan sha, da abinci, tallafin da kakakin MDDr ya ce an fi karfafa shi, a kananan cibiyoyin kiwon lafiya dake yankunan dake kan iyakar Malin da kasar Guinea. (Saminu)