A ranar Jumma'a 21 ga watan nan ne hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da cewa, yanzu haka babu sauran mutane dake dauke da kwayar cutar Ebola a kasar Congo (Kinshasa), sakamakon nasarar yakin da aka yi da cutar.
Wata sanarwar da hukumar ta WHO ta fitar a birnin Geneva, ta bayyana cewa, a ranar 20 ga watan nan na Nuwamba, aka cika kwanaki 42 da sallamar mutum na karshe dake dauke da cutar ta Ebola daga asibiti, bayan da aka yi masa gwaji har sau biyu, aka kuma tabbatar ya warke sarai.
Bisa sharuddan hukumar WHO dai sai an kwashe kwanaki 42 da samun bullar cutar ta Ebola a karo na karshe, za a iya tabbatar da rashin cutar baki daya.
Hukumar WHO dai ta jinjinawa mahukuntan kasar ta Congo, bisa kokarin dakile yaduwar wannan cuta, da kuma irin goyon baya da suka baiwa sassa daban daban wajen wannan aiki, ciki had da kafa tawagar masana cikin hanzari, da tabbatar da lura da wadanda suka yi mu'amala da masu dauke da cutar, da ba da jagoranci wajen binne mutanen da cutar ta hallaka.
Har wa yau hukumar ta jaddada muhimmancin rawa da shugabannin addinai da na al'umma suka taka wajen shawo kan barkewar cutar ta Ebola.
A daya hannu kuma, sakamakon raunin da gwamnatin Congon Kinshasa ke da shi, mahukuntanta, da hukumar WHO sun fahimci muhimmancin ci gaba da taka tsan-tsan matuka, wajen sa ido kan barkewar cututtuka masu saurin yaduwa a dukkanin fadin kasar. (Tasallah Yuan)