Ya zama wajibi gwamnatin kasar Mali ta rufe kan iyakarta tare da kasar Guinea ta garin Kouremale har tsawon a kalla wata daya, in ji Soumaila Cisse, shugaban jam'iyyar URD, babbar jam'iyyar adawa ta kasar Mali a ranar Laraba. Ya ba da hujjar wannan sha'awar tasa, a yayin wani taron menama labarai, bisa dalilin cewa, dukkan masu fama da cutar Ebola a kasar Mali sun fito daga kasar Guinea, kasar da ta fi fama da cutar Ebola. Wannan na nuna cewa, babu wani binciken da ake sosai. Don haka akwai bukatar rufe iyaka da kasar Guinea ta garin Kouremale a tsawon a kalla wata daya, in ji mista Cisse. A ra'ayinsa, wannan rufe ta 'dan lokaci za ta baiwa ma'aikatan lafiya damar samun kayayyakin aiki da shiryawa yadda ya kamata, abin da a halin yanzu ba haka ba. (Maman Ada)