Cibiyar kula da shigowar baki da kasancewar zama 'dan kasa ta Liberiya ta bayyana a ranar Laraba cewa, iyakokin kasa na kasar tare da kasashen Guinea da Saliyo za su cigaba da kasancewa rufe domin samun damar takaita yaduwar cutar Ebola.
Shugaban cibiyar, kanal Abraham Dolley, ya tabbatar da haka a gidan rediyon tawagar MDD dake Liberiya (UNMIL) cewa, ba za'a bai wa mutum guda iznin shiga Liberiya ba tun daga kasashen makwabta daga tashoshin shige da ficen jama'a. Kanal Dolley ya nuna cewa, wannan matakin na da manufar hana yaduwar cutar Ebola daga kasashen makwabtan Liberiya. Haka kuma ya tabbatar da cewa, wasu mutane sun shigo kasar ta barauniyar hanya ba tare da an yi musu gwajin cutar Ebola ba, lamarin dake kara dagule kokarin gwamnatin kasar wajen yaki da cutar Ebola. (Maman Ada)