Gidan talebijin na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaba Rohani ya fadi hakan ne yayin da yake ganawa da jakadan kasar Norway dake kasar Iran Odyssey Norheima a wannan rana.
Amma a sa' daya kuma shugaba Rohani ya jaddada cewa, shirin nukiliya da kasar Iran ke gudanarwa bai sabawa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ba. Kana tana gudanar da shi ne a karkashin sanya idon da hukumar IAEA ta yi. Sa'an nan ya nanata cewa, kasarsa na da hakkin yin amfani da makamashin nukiliya cikin zaman lafiya.
Bugu da kari, kamfanin dillancin labaru na kasar Iran IRNA ya ruwaito mamban tawagar Iran a shawarwarin yana cewa, labarin da aka bayar cewa wai Iran tana duba yiwuwar tsawaita lokacin yin shawarwarin ba gaskiya ba ne. Ya ce, a halin yanzu, bangarori daban daban suna nuna sahihanci ga shawarwarin, kana suna fatan za a kammala shawarwarin kafin ranar 24 ga watan Nuwanba. (Zainab)