A yayin da yake zantawa da wakilan kamfanin dillancin labarun kasarsa, ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa, a yayin shawarwarin kasarsa ta tsaya kan matsayinta na amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, ta kuma jaddada cewa, al'ummar Iran ba za su sadaukar da hakkinsu a wannan fanni ba.
Bayan shawarwarin wani babban jami'in kasar Amurka ya nuna cewa, burin kasarsa shi ne, cimma wata yarjejeniya a cikin wa'adi wato kafin karshen watan Nuwamba.
A nasa bangare babban wakilin kasar Rasha kan batun shawarwarin, Sergei Ryabkov a wannan rana ya bayyana cewa, babban burin da ake fatan cimmawa kan shawarwarin, shi ne daddale wata yarjejeniya ta dogon lokaci, wadda za ta samu amincewar sassan da ke halartar shawarwarin. (Bilkisu)