in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran da kasashe shida sun cimma shawarwarin zagayen karshe kan shirin nukiliya na Iran
2014-09-27 17:07:26 cri
Kasar Iran da manyan kasashe shida sun cimma a ranar Jumma'a a birnin New-York zagaye na bakwai na shawarwari kan shirin nukiliya na Iran.

Dukkan bangarorin sun amince da shirya zagayen karshe na shawarwari da zaran dama ta samu, in ji Wang Min, shugaban tawagar masu tsakani na kasar Sin.

A cewar mista Wang, dukkan bangarorin sun nuna, a lokacin tattaunawar, niyyarsu ta siyasa wajen cimma wata yarjejeniya ta baki daya nan da gajeren lokaci da kuma gudanar da shawarwari kan muhimman batutuwa, kamar tace sanadirin uranium bisa tushen gaskiya da ci gaba da kuma duba hanyoyin amsa damuwar dukkan bangarorin.

Zaman taron shawarwarin da aka kawo karshensa tsakanin Iran da kasashe shida wato Amurka, Rasha, Burtaniya, Faransa, Sin da Jamus, an fara shi yau da mako guda. Baya ga wakilan manyan kasashen shida, shugabar diplomasiyyar tarayyar Turai, Catherine Ashton da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Javad Zarif na daga cikin mahalarta taron.

Mista Wang ya yi alkawarin kuma cewa kasar Sin na shirye wajen aiki tare da dukkan bangarorin da abun ya shafa da kuma ci gaba da kokarin da za su taimakawa wajen bullo wata yarjejeniyar gaskiya, bisa adalci, kuma bisa moriyar juna. (Maman ADA)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China