A kuma Lahadin dake tafe ne kungiyar ta Manchester United za ta buga wasa da Arsenal, a ci gaba da buga gasar Premier League, wasan da ake hasashen cewa idan har 'yan wasan kungiyar da keda raunuka basu warke ba, na iya baiwa Manchester ruwa.
Daya daga irin wadancan 'yan wasa na Manchester dake fama da jiyya Daley Blind, ya samu matsala ne ya yin wasan da ya bugawa kasar sa wato Netherlands a karawar su da Latvia. A ya yin wannan wasa Blind ya buga wasa ne na tsawon mituna 20 kacal kafin a canza shi saboda raunin da ya samu.
A cewar babban kocin kungiyar kasar ta Netherlands, Blind ya ji rauni ne a kokon gwiwar sa. Kuma mai yiwuwa ne ya yi huta har tsawon makwani 4 zuwa 6. Blind kari ne kan 'yan wasan na Manchester United masu jiyya, domin kafin sa Micheal Carrick da David de Gea su ma sun shiga hutun jiyyar raunukan da suka samu.
Ragowar 'yan wasan na Manchester United dake fama da rauni sun hada da Marcos Rojo, da Ashley Young, da Jesse Lingard, da Rafael, Phil Jones, da Radamel Falcao da kuma Jonny Evans. Kuma sanannen al'amari ne cewa wadannan 'yan wasa 10 na iya zama wani rukuni mai karfi da ke iya wakiltar kungiyar ta Manchester United a fagen taka teda.
Rahotanni dai sun bayyana cewa Blind shi ne dan wasa mafi muhimmanci ga kungiyar cikin dukkanin 'yan wasan na ta masu rauni, kuma rashin sa na iya haifarwa kungiyar gagarumar matsala.(Zainab)