141030-kungiyar-kwallon-kafar-najeriya-ajin-mata-ta-lashe-kofin-afirka-zainab.m4a
|
Gasar dai ta bana wadda aka kammala a ranar Asabar a birnin Windhoek na kasar Namibia, ta kasance ta 9, tun bayan da aka fara gudanar da gasar ajin na mata.
'Yan wasan kungiyar Super Falcons Desire Oparanozie, da Asisat Oshoala ne dai suka jefa kwallaye biyun da suka baiwa Najeriyar nasarar da ta samu a wannan karo.
Najeria ce dai ta fi daukar wannan kofi tun bayan kaddamar da shi a shekarar 1998, domin kuwa sau biyu kacal ta rasa nasarar daukar sa, tun da aka fara buga gasar. Wato dai kulaf din na Super Falcons ya lashe wannan kofi har sau 6, inda kasar Equatorial Guinea ta dauka sau biyu a shekarun 2008 da 2012.
A yanzu haka kuma kungiyar ta Super Falcons ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ajin mata da za a buga badi a kasar Canada, inda kuma za ta wakilci Afirka tare da kasashen Kamaru da Cote D'Ivoire.(Saminu Alhassan)