in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Manchester United tana fuskantar koma baya
2014-10-17 16:42:39 cri

Sanin kowa ne cewa, shahararriyar kungiyar kwallon kafan nan ta kasar Birtaniya wato Manchester United ba ta yi nasara sosai ba a kakar wasa ta shekarar 2013 zuwa ta 2014 karkashin jagorancin tsohon kocin kungiyar David Moyes. Sai dai a kakar wannan wasa bayan da Louis Van Gaal ya zama sabon kocinta, kungiyar ta ci gaba da fama da matsalar kasa tabuka abin azo- a gani a wasanninta.

Idan mun dubi tarihin kungiyar Manchester United, za mu ga cewa yadda kungiyar ta sha kashi a karawarta da Leicester City a ranar 21 ga watan Satunban bana shi ne abin kunyan da ba ta taba ganin irinsa ba a tarihi, ganin yadda kungiyar ta fara zura kwallaye 2, amma daga bisani reshe ya juye da mujiya inda Leicester City ta doke Man. United da ci 5 da 3 a karshe.

Baya ga nasarar da Leicester City ta yi a wannan wasa, dalilin da ya sa ganin yadda Leicester City ba ta dade da shiga gasar Premier ba, sa'an nan a shekaru 20 da suka gabata, kungiyoyi 6 ne kawai suka taba zura kwallaye 5 cikin ragar Man. United, amma yanzu Leicester City ta kasance daya daga cikinsu, duk da cewa ba wata kungiya ce mai karfi ba.

Idan mun koma shekara ta karshe da Alex Ferguson ya yi yana aiki a Manchester United wato kakar wasa ta shekarar 2012 zuwa ta 2013, za mu ga yadda wannan kungiya ta canza yanayin wasa a karawa guda 10, wato yayin da abokan karawarta suka zura mata kwallaye, amma daga baya kungiyar Man. United ta fara sheda karfinta bisa cin kwallaye a jere da samun nasara a karshen wasan. A lokacin ma iya cewa kungiyar Man. United ta kasance 'sarkin canza yanayin wasa', amma yanzu ta zama kungiyar da aka fi dagula mata lissafi.

A wannan kakar wasan mun ga yadda kungiyar Swansea City ta lashe Man. United a wasanta na farko. Sa'an nan a yayin karawarta da kungiyar Sunderland, duk da cewa Man. United ce ta fara zura kwallo 1, amma daga bisani Sunderland ta rama cin da aka mata inda suka yi kunnen doki a karshe. Daga baya sai shan kashin da ta yi a karawarta da Leicester City, inda aka ci ta kwallaye 4 a jere cikin mintuna 4. Don haka ma iya cewa, Man. Uniteda ta rasa tagomashinta tun bayan da Ferguson ya bar kungiyar.

Amma game da wasan da Man. United ta buga da Leicester city, wasu kafofin watsa labaru sun ce alkalin da ya jagoranci wasan Marc Sternberg shi ne mai laifi wanda rashin adalcinsa ya sa kungiyar Man. United ta sha kasha a wannan karawa. An ce, yayin da dan wasan bayan kungiyar Rafael Da Silva yake kokarin tare Jamie Vardy, an yi masa keta, amma Sternberg bai yi hukunci a kai ba. Daga bisani yayin da Rafael ya kama ketar da Vardy ya yi masa, sai alkalin wasa Sternberg ya yi masa hukunci, ya sa aka baiwa abokan karawar Man. United bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Hakika a da Man. United ta taba samun fifiko a wasan da Sternberg ya jagoranta. A kakar wasa ta 2012 zuwa ta 2013 yayin da Man. United ta kara da Chelsea, Sternberg ya nuna baiwa Ivanovic da Torres na kungiyar Chelsea jan kati, sa'an nan ya kau da ido yayin da Hernandez na Man. United ya ci kwallo da ake ganin ta saba doka, lamarin da ya sanya Steven Howard na jaridar 'the Sun' ya ce Sternberg ya maye gurbin Howard Webb na zama 'alkalin wasan da ke goyon bayan kungiyar Manchester United'. Amma a wannan karo, mun ga yadda Sternberg ya juya baya ga Man. United.

Tun bayan da Ferguson ya bar Man. United,sai alkalan wasa suka fara juya wa kungiyar baya. A karawar da Man. United ta yi da Liverpool, Sternberg ya ba liverpool damar bugun daga kai sai mai tsaron gida har karo 3, lamarin da ake ganin ba zai taba faruwa ba a zamanin Ferguson. Hakika a wasanni 6 da Man. United ta buga wanda kuma Sternberg ya yi alkalanci, ya baiwa 'yan wasan Man. United 3 jan kati, kana ya baiwa abokan karawar kungiyar damar bugun daga kai sai mai tsaron gida 5.

Alkaluma sun nuna cewa, cikin shekarar 2014 kawai, an yi wa kungiyar Man. United bugun daga kai sai mai tsaron gida sau 6, adadin da ya zama daya da na Hotspur, adadi mafi yawa a teburin gasar Premier. Sai dai yayin da alkalan wasa suke aikata kuskure tare da tallafawa abokan karawarsa, Van Gaal bai tabuka kome ba, face nade hannu yana kallo a bayan fili. Ko da yake kyaftin din kungiyar Wayne Rooney ya daga murya don neman karfafa wa abokan wasansa kwarin gwiwa, koda ya ke shi ba kamar sauran fitattun 'yan wasa irinsu Roy Keane da Gary Neville ba ne, don haka da wuya zai iya canza yanayin da ake ciki.

Yadda Manchester United take dinga shan kashi, ya sa masu goyon bayan kungiyar bakin ciki da bacin rai. Kamar yadda Gary Neville dake sharhi a tashar gidan telabijin na Sky Sports ya bayyana, cewa 'Kungiyar Man. United ba ta da karfi. Ta yaya za ta iya lashe kofi? Ya kamata ta yi koyi da fasahar Chelsea da Man. City domin su ne kungiyoyi masu karfi.' Kuma a nasa bangaren, jakadan Man. United Bryan Robson ya dan kare matsayin kungiyar da cewa 'yadda take kai hari babu matsala,amma tana da matsala sosai a fannin tsaron gida'.

Mun san da ma a filin wasanta na Old Trafford, Man. United ta samu nasarori da yawa, domin abokan karawarta su kan firgita sosai ganin karfin kungiyar da wani yanayi da ta kan nuna na kasancewa a gida. Amma a shekarun baya mun ga yadda Man. United ta sha kashi sosai ko da a wasannin da ta yi gida

Watakila barin Ferguson shi ma ya yi tasiri a wannan fanni, domin tsohon alkalin wasa Graham Poll ya taba tona asirin lamarin cewa, Ferguson ya kan matsawa alkalan wasa lamba sosai, ko idan ya zare musu ido shima zai yi musu tasiri. Sa'an nan yayin da ya yi magana dangane da alkalan wasa a gaban 'yan jarida, dukkan alkalan wasa su kan ji dar-dar a zuci. Kana suna tsoron yanke hukuncin bugun daga kai sai mai tsaron gida a filin wasan Manchester.

Sai dai barin Ferguson ya raunana kungiyar Manchester United sosai, ganin yadda kungiyar ta sha kashi a wasanni 7 da suka gudana a filin wasanta na Old Trafford a kakar wasa ta 2013 zuwa ta 2014, abin da ya sanya masu kaunar kungiyar begen tsohon babban kocinta Alex Ferguson sosai. A cewarsu, idan Ferguson yana nan, ba zai yarda Swansea City, Milton Keynes da dai sauransu su bata sunan kungiya Manchester ba.

Hakika Ferguson ya kwashe shekaru fiye da 20 yana kokarin raya kungiyar Mancheter United. Ya ba kungiyar lakabin 'fadar Allah', kuma, shi da kansa ya zama tamkar 'mai kare wannan fadar. Sannan da wuya a iya raba shi da kungiyar Manchester United, ganin halayyarsu kusan iri daya ne.

Idan Ferguson ya tsaya a gefen filin wasa, ba zai yiwu ba a yanke wa kungiyar Manchester hukuncin bugun daga kai sai mai tsaron gida har sau 6 a shekarar 2014 kadai ba. Domin idan ya ga ana neman yanke wani hukuncin da bai dace ba ga kungiyar, ko kuma ba a bayar da isashen karin lokaci a karshen wani wasa ba, ya kan yi fushi sosai, kuma zai fara nuna yatsa ga alkalan wasa da sauransu.

Wannan mataki nasa yana tasiri ga 'yan wasan da kuma kungiyar Manchester United baki daya, sannan mun ga yadda ya yi amfani da kwarjininsa don horar da 'yan wasa, har ma ya kan yi wa 'yan wasansa fada a yayin hutun rabin lokaci. Kamar yadda Juan Veron ya bayyana cewa, shi Ferguson kamar wani kwamanda ne a cikin kungiyar Manchester United, wanda ya kan ba sauran mutane tsoro. An ce, fitattun 'yan wasa kamarsu Beckham, Philip Neville, Paul Scholes dukkansu suna tsoronsa sosai. Haka kuma, Ferguson ba zai yi hakuri idan an samu rikici tsakanin 'yan wasan kungiyar ba. Amma bayan da Ferguson ya tafi, kuma Moyes da Van Gaal sun maye gurbin sa, sai aka fara samun rikici sosai tsakanin 'yan wasan Manchester.

Hakika a kakar wasan da ta gabata, Moyes ya bayyana takaicinsa cewa, ko da Ferguson ya dawo horas da kungiyar, watakila sakamakon da aka samu ba zai kai na yanzu ba, ma'ana wato kungiyar na fuskantar matsaloli da yawa yanzu. Sa'an nan a nasa bangare Van Gaal shi ma ya bayyana cewa, ba bu tsari a kungiyar, ganin yadda 'yan wasa da yawa suna da matsayi daya, kana ba a samun daidaituwa tsakanin 'yan wasan gaba da na baya.

Maganarsu gaskiya ce, idan aka yi la'akari da yadda Ryan Giggs ya yi ritaya a wannan lokacin zafi, kana Ferdinand da Nemanja Vidic su ma suka bar kungiyar. Daga bisani shima Patrice Evra ya bar kungiyar inda ya koma kungiyar Juventus. Ta haka kungiyar ta kusan rasa dukkan fitattun 'yan wasan bayanta. Sa'an nan kungiyar matasa ta Manchester United ita ma ta kasa samar da taimakon da ya dace ganin yadda fitattun 'yan wasa kamarsu Danny Welbeck da Thomas Cleverley su ma sun sauya sheka. Yanzu haka kungiyar Manchester United bata da wani dan wasan da zai maye gurbin Giggs a matsayin shugabanta, kuma ba ta da fitattun 'yan wasa matasa, gaskiya ta sha bamban da Manchester Unied da muka sani a da.

Kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya sun taba bayani kan wasu abubuwa dake alamanta al'adun musamman na kungiyar Manchester United, wadanda suka hada da hadarin jirgin sama da ya abku a birnin Munich a shekarar 1958, wanda ya kashe 'yan wasan kungiyar da yawa, lamarin da ya tunasar da 'yan wasanta cewa kada su manta da tarihi, kuma kada su yi sanyin gwiwa a duk matsalar da suke fuskanta.

Gami da 'zuriyar zinariya' lakabin da aka yi wa fitattun 'yan wasan kungiyar a shekarar 1992, abin da ya alamanta yadda kungiyar take mai da hankali kan horar da 'yan wasa matasa, da sanya su su gaji halayyar magabatansu.

Sai dai a wannan zamani da ake kokarin saye da sayar da 'yan wasa, da kokarin neman samun riba ta fuskar wasanni, sannu a hankali an rasa wadannan halaye na musamman na kungiyar Manchester United, ganin yadda kulob din ya fara zama kamfani, kana a kan alakanta sakamakon wasanni da darajar 'yan wasa a kasuwa. Don haka, a wannan zamani babban kocin kungiyar yana samun matsin lamba sosai, domin idan kungiyar ta kasa sheda karfinta a wasu wasanni, to, za a iya korar kocinta. Don haka, yanzu da wuya a samu wani kocin da zai yi shekaru fiye da 20 yana aiki a wata kungiyar kamar yadda Ferguson ya yi.

Ko da shima Ferguson, ya amince da ra'ayi na raya wasan kwallo kafa da kudi a karshen aikinsa a matsayin koci. Saboda haka ya kashe makudan kudi don sayen Anderson Oliveila, Nani, Wayne Rooney, da Van Persie, da Berbatov, ta yadda ya samu damar kiyaye ysarin da mutuncin kulob dinsa, gami da tabbatar da ganin kungiyar ta yi nasarori a wasanni daban daban.

Hakika tsarin kungiyar Manchester United shi ne abin da Ferguson ya kwashe shekaru fiye da 20 yana kokarin kiyaye wa, don haka ya zama kashin bayan kungiyar da ya dade yana kasancewa. Duk da cewa yanzu Van Gaal ya dawo kungiyar, amma da wuya zai iya canza tsarin cikin gajeren lokaci.

Mun san Ferguson bai mai da hankali kan wasu sabbin fasahohi sosai ba, domin a ganinsa an samu nasara ne ba domin daukar wata fasaha ta musamman ba, sai domin kokarin da 'yan wasa suka yi. Don haka ya kan dauki wasu tsoffin fasahohin kasar Birtaniya, kamar yadda ya sanya 'yan wasan gaba 4, da 'yan wasan tsakiya 4, da na baya 2 a lokacin karawa.

Yanzu wannan fasahar ta riga ta tsofa, kana matasa 'yan wasan kungiyar Manchester United ba su fara sheda karfinsu sosai ba tukuna, haka kuma sauran kungiyoyi kamarsu Chelsea da Man. City su taso, abun da ya kara sanya kungiyar Manchester United cikin wani yanayi na tsaka mai wuya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China