in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid mai kyasar taurarin 'yan wasa
2014-09-30 09:05:58 cri

Jama'a idan ba ku manta ba, a zagaye na 2 na gasar La Liga, Real Sosiedad ta lashe Real Madrid da ci 4 da 2, abun da ya zama babbar koma baya ga Real Madrid, bayan da ta ci tura a kokarin rike kambi a gasar Supercopa de Espana. Ganin haka ya sa marubuta labaran wasanni ke zargin shugaban kulob din Real Madrid Florentino Perez da wuce gona da iri, ta la'akari da yadda yake kokarin tattara fitattun 'yan wasan gaba maimakon masu tsaron gida.

A wannan kakar sayar da 'yan wasa, Perez ya sayar da Angel di Maria a kan kudin Euro miliyan 75,sai Alvaro Morata da aka sayar a kan kudi Euro miliyan 20, ta yadda zai samu isasshen kudi don sayen James Rodriguez, wanda tauraronsa ya haskaka sosai a gasar cin kofin duniya da ta gudana a Brazil. Sai dai lamarin ya canza tsarin 'yan wasan kulob din sosai , musamman ma bisa la'akari da yadda Xabi Alonso ya bar kungiyar ba zato ba tsammani.

Bayan da Alonso ya tafi, sai Toni Kroos, wanda shi ma dan wasan tsakiya ne, ya maye gurbinsa. Mun san Kroos yana da kwarewa wajen raba kwallo da kuma gudu, amma bai kai Alonso daidaita wasan tsakiya da kuma tsaron gida ba. Da ma Alonso shi ne dan wasan dake jagorantar kai hari da tsaron gidan kulob din Real Madrid, kuma shi ke tsara yadda yanayin wasan zai kasance, ta yadda za su samu saukin doke abokan karawarsu. Dan wasan mai shekaru 32 a duniya ya shafe shekaru fiye da 10 yana taka kwallo a wannan matsayi. Yanzu duk da cewa kulob din bai sayar da Sami Khedira ba, amma hakan ba zai warware matsalar da barin Alonso ya haddasa ba.

Idan mun koma wasan da aka buga tsakanin Real Madrid da Real Sociedad, za mu ga Madrid ta fara da kokarin kai hari, kana ta samu maki 2 cikin sauki, amma yadda 'yan wasanta suke kokarin ganin sun samu maki ya sa kungiyar ta tsunduma cikin wani yanayi mai hadari. Kungiyar na bukatar kwantar da hankulan 'yan wasanta, da daidaita yanayin wasan yadda ya kamata, musamman ma lokacin da Sociedad ta rama kwallo daya. Idan da Alonso yana buga wa kungiyar a wannan lokaci, zai iya jagorantar 'yan wasan baya, gami da tallafawa Kepler Ferreira da Sergio Ramos wajen tsaron gida, watakila Real Madrid ba za ta sha kashi a wancan wasa ba.

Za mu iya ganin kwarewar Alonso ta hanyar zayyana rawar da ya taka a kakar wasan 2013 zuwa 2014. Bayanai na cewa, a ko wane wasa, Alonso ya kan kwace kwallaye 2.4, daga dan wasan da ke kai musu hari karo 1.5, gami da murkushe harin da aka kai musu karo 1.6, kwazon da ya dara na Toni Kroos. Hakan ya sheda cewa shi Alonso ya iya tsaron gida sosai. Yanzu babu Alonso a matsayin 'yan wasan tsakiyar da ke bugawa Real Madrid, ana iya keta Ramos da Ferreira kai tsaye, lamarin da ya kan sa su sha kaye sosai.

A wannan kakar sayar da 'yan wasa, Perez ya ware Euro miliyan 80 don sayen J. Rodriguez, kana ya kashe Euro miliyan 30 don sayo Kroos, da biya Euro miliyan 10 don shigo da Navas, baki daya kudin da ya kashe ya kai Euro miliyan 120. Sa'an nan a wani bangare na daban, Perez ya sayar da Di Maria, Morata, Nuri Sahin da Alonso, inda ya samu Euro miliyan 110.

Domin sayen James Rodriguez, an sayar da kwararrun 'yan wasa 2 gami da dan wasan da ya kan zauna a benci, lamarin da ya kayyade yawan 'yan wasan jerin farko na Real Madrid zuwa 21 kawai. Hakika ban da wasu 'yan wasa matasa wadanda taurarinsu ba su fara haskewa ba tukuna, 'yan wasan da babban kocin kungiyar Carlo Ancelotti ya kan yi amfani dasu a wasanni ba su wuce mutane 19 ba. Sa'an nan cikin 'yan wasan da su kan zauna a benci akwai Khedira,Arbeloa, Ignacio, Illarramendi, da Varane, amma cikinsu babu wanda zai iya jagorantar sauran 'yan wasan kungiyar.

Bayan da Morata ya bar Real Madrid, Benzema ne ya zama dan wasa daya kadai da ya rage a kungiyar da ya ke buga wasan gaba da tsakiya. Ganin wannan yanayi da kungiyar ta shiga, ya sa Perez ya nuna sha'awar dauko Javier Hernandez na Menchester United. Sakamakon manufar kulob din na sayan manyan taurari ne ya sa ta tsunduma cikin wannan yanayi mai wuya, ganin yadda ba za ta sayar da 'yan wasa da dama tare da canza tsarin kunigyar sosai ba, in ba domin sayo James Rodriguez wanda ya shahara a fagen wasan kwallon kafa ba.

Amma abin da ya fi addabar kungiyar shi ne yadda ta kasa samun isassun 'yan wasan baya. Idan aka yi la'akari da salon wasan Real Madrid na yawaita kai hari daga bangare daban daban, kamata ya yi kungiyar ta kiyaye 'yan wasan baya na tsakiya 4. Sai dai yanzu 'yan wasan baya na tsakiya da Ancelotti ke da su 3 ne kawai, wato Ramos, Ferreira, da Varane, yayin da Varane ya taba jin rauni mai tsanani, har yanzu bai farfado sosai ba. Don haka kungiyar Real Madrid na da 'yan wasan baya na tsakiya 2 kawai wadanda za a iya dogaro kansu.

Idan aka hada da 'yan wasan baya na gefuna 2, za a ga cewa,dukkan 'yan wasan bayan kungiyar sun kunshi Ramos,Ferreira, Carvajal, Marcelo, da Coentrao. Sai dai wadannan 'yan wasan su ma suna son kai hari da neman zura kwallo a raga, don haka ba sa iya kare bayan kungiyar sosai idan ba su samu tallafi daga 'yan wasan gaba da na tsakiya ba.

Wannan yanayin da Real Madrid ke ciki yana da alaka sosai da sha'awar da kungiyar ta kan nuna a fannin musaya ,saye ko sayar da 'yan wasa. A ko wane kakar sayar da 'yan wasa, Kulob din ya kan canza 'yan wasansa da yawa, a kokarin samun fitattun 'yan wasa masu tsada matuka. Sai dai duk lokacin da kungiyar ta samu wani kwararren dan wasa, ta kan yi kokarin rubuwa da wani tsohon kwararren dan wasanta.

Ga misali a kakar sayar da 'yan wasan da ta gabata, Real Madrid ta ware Euro miliyan 100 don sayen Gareth Bale, yayin da ta sayar da Mesut Ozil ga Arsenal a kan kudi Euro miliyan 50. A shekararsa ta farko da yake taka kwallo a Arsenal, Ozil ya zama dan wasan tsakiya dake jagorantar kungiyar. Sa'an nan a wannan kakar sayen 'yan wasa, Real Madrid ta sayo James Rodriguez yayin da ta sayar da di Maria, duk da cewa di Maria ya taba taka rawar gani a gasar cin kofin zakarun Turai. Bayan da Di Maria ya koma Mancheser United ya taimakawa kungiyar sosai.

A nasa bangaren,Alonso ya fara taka leda 'yan lokuta kadan bayan da ya sauya sheka zuwa Bayern Munich, lamarin da ya sanya shi samun yabo sosai. Ta haka za a iya ganin cewa, 'yan wasan da Real Madrid ta rabu da su dukkansu na da kwarewa sosai, kamar su Wesley Sneijder, Arjen Robben, Ozil, da Di Maria, da dai sauransu.

Bayan da Robben da Sneijder suka bar Real Madrid, dukkansu sun taba zama zakaru a gasar lig-lig da suke buga wa a kungiyoyinsu. Kana Ozil shi ma ya taba taimakawa Arsenal don ta sake zama zakara a gasar firimiya bayan ta taba lashe kofin a shekaru 8 da suka wuce. Hakika idan mun dubi tarihin kungiyar Real Madrid, za mu gano cewa kungiyar ta kan samar da kwararrun 'yan wasa ga sauran kuloflika, tun bayan da Perez ya fara daukar matakan shigo da fitattun 'yan wasa a shekaru fiye da 10 da suka wuce.

Ga misali a kakar wasa ta shekarar 2003 zuwa ta 2004, Real Madrid ta sayar da Claude Makelele, abin da ya fara sanya ta shiga matsala sosai. Shi dai Makelele ya dawo Real Madrid ne a shekarar 2000, inda ya yi kokarin tallafawa Zidane da Figo, tare da ba da gudunmowa a fannin tsaron gida. Bisa kokarinsa ne, manufar Perez ta dogaro kan Zidane da Pavon ta yi amfani, ta yadda kungiyar Real Madrid ta samu damar lashe kofin zakarun nahiyar Turai. Sai dai a shekarar 2003 Perez ya sayi Beckham wanda ya fara taka leda a matsayin dan wasan tsakiya, don haka ya maye gurbin Makelele.

Amma bayan da Makelele ya tafi Chelsea, manufar Perez ta dogaro kan hadin gwiwar Zidane da Pavon ta daina amfani, abin da ya sanya Real Madrid ta kasa lashe kowace gasar da ta shiga a shekaru 3 a jere. Har ma ta sauko zuwa matsayi na 4 a gasar La Liga a kakar wasa ta 2003 zuwa ta 2004, inda a karshen kakar ta sha kashi sau 5 a jere.

Dangane da sallamar Makelele da aka yi, Zidane ya ce, 'yanzu kashin bayan kungiyar ba ya nan, ko za a iya maye gurbinsa?' Shi ma Casillas ya bayyana yadda yake begen Makelele da cewa, 'idan za a bar ni na zabi mutum daya da zai kasance tare da ni a baya na fi son Makelele, maimakon Zinane, Ronaldo, ko kuma Beckham,.'

Hakika wannan ba shi ne karo na farko da Real Madrid ta yi wa kanta barna ta hanyar sayar da 'yan wasanta, ga misali, duk a shekarar 2003, sakamakon yadda Ronaldo ya yi kane-kane a matsayin dan wasan tsakiyar kungiyar daya dilo, ya sa Morientes ya bar Real Madrid don zuwa Monaco. Sa'an nan a wasan dab da kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2003 zuwa 2004, Real Madrid ta kara da Monaco. Abun da ya biyo baya na san masu sha'awar wasan kwallon kafa da yawa za su iya tunawa da shi, wato Real Madrid ta doke Monaco da ci 4 da 2 a wasa na farko, sa'an nan a karawarsu ta 2 Monaco ta rama inda ta lashe Real Madrid da ci 3 da 1.

Bisa jimillar kwallaye a karshe, Monaco ta samu damar zuwa zagaye na gaba,bayan da Real Madrid da ta sha kaye. Amma dan wasan Monaco da ya fi taimakawa a wannan wasa Shi me Morientes, inda ya zura kwallo a raga a dukkan wasannin 2, gami da tallafawa abokan kungiyarsa samun maki. Ganin yadda tsohon dan wasanta ya taimaka wajen doke ta a lokacin gasa mai muhimmanci, wannan ya kasance abin kunya ga Real Madrid.

A wani bangare na daban, yayin da Real Madrid take kokarin samun fitattun 'yan wasa wadanda taurarinsu ke haskakawa sosai a halin yanzu, a hannu guda kuma ta kan rabu da tsoffin 'yan wasanta, duk da cewa sun taba taimaka mata samun nasarori da yawa. Ga misali, tsohon kyaftin din kungiyar Fernando Hierro ya shiga kungiyar a shekarar 1989, wanda ya dade yana taka rawa a matsayin mai jagorantar kungiyar bisa halayyarsa mai nagarta.

Cikin shekaru 14 da ya shafe yana taka leda a Real Madrid, Hierro ya buga wasanni 601 da kungiyar,inda ya tallafa mata a kokarinta na lashe kofin gasar La Liga 5, da kofin zakarun Turai 3. Amma duk da haka bayan da wa'adin kwagilar Hierro ta cika a shekarar 2003, Perez ya ki tsawaita kwangilar shekara guda da kungiyar, abun da ya tillasta Hierro barin kungiyar.

Ban da Hierro, wasu tsoffin 'yan wasan kamarsu Raul Gonzales da Jose Gutierrez dukkansu sun sanar da barin Real Madrid a kwana guda a shekarar 2010. Ganin hawayen da tsoffin 'yan wasan suka yi ya sa masu kaunarsu bakin ciki sosai. Don haka, ana iya ganin cewa, zai yi wuya sosai idan wani tsohon dan wasa ya ci gaba da taka leda a kungiyar Real Madrid, wadda a kullon take neman sabbin jini.

Game da dalilin da ya sa Perez yake kokarin neman fitattun 'yan wasa, wasu manazartar harkokin wasanni sun ce, hakika ya yi haka ne ba domin neman kara karfin kungiyar Real Madrid kawai ba, wani abun da ya fi mai da hankali a kai shi ne kokarin sanya kungiyar ta janyo hankalin masu sha'awar wasan kwallon kafa.

Kowa ya san cewa,Perez babban dan kasuwa ne, wanda ke da kamfani na gini. Don haka, ya fahimci cewa yadda ake kara janyo hankalin mutanen duniya zai sa kulob dinsa ya dinga samun nasarori a fannin kasuwanci, ko da ya yi nasara a filin wasa ko ya sha kaye.

Bisa wannan dabarar da shugaban kungiyar Real Madrid ke amfani da ita,ta sanya kulob din dade wa a matsayin kulob da ke kan gaba wajen samun kudi da yawa a duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China