in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Baxy na fatan kammala kakar wasannin bana da kyakkyawan sakamako
2014-10-31 10:13:06 cri
Ya yin da ake daf da kammala gasar kwallon kafar ta China League a kakar wasannin bana, kungiyar wasan kwallon kafa ta Baxy dake nan birnin Beijing, ta jawo hankalin masu sha'awar tamaula, bayan da ta cimma lashe wasanni 21 a jere.

Babban kocin kungiyar Goran Tomic dan kasar Croatia ya bayyana cewa kungiyar ta riga ta samu sakamako mai gamsarwa, kana tana fatan kammala kakar wasannin ta bana da kyakkyawan sakamako, a shirin ta na tunkarar wasannin shekarar badi.

Kafin bude kakar wasannin ta shekarar 2014, kungiyar ta Baxy ta bayyana burinta na zama a matsayin dai ba zai yi kasa da shida ba a kakar wasannin ta bana. Amma babu wanda ya yi hasashe cewa kungiyar za ta samu nasarori masu yawa a jere, har ta lashe wasanni da dama a jere a wannan kaka.

Game da hakan Tomic ya bayyana cewa, kungiyar da yake horaswa na fatan kammala kakar da kyakkyawan sakamako, tare da kiyaye matsayin ta na hudu ko na biyar a karshe.

A hakika dai, kungiyar Baxy tana samun ci gaba a kowace shekara. Inda a kakar wasanni ta shekarar 2013, kungiyar ta dare matsayi na 7 a karshen gasar China League, kuma wannan ne sakamako mafi kyau da ta samu a tarihin ta. A kakar wasanni ta bana kuwa, ya zuwa yanzu babu shakka matsayin kungiyar ya daga bisa na bara. Nasarar lashe wasanni 21 a jere da kungiyar Baxy ta samu a dandalin wasan kwallon kafa na kasar Sin, ya haska ta a idon duniya, tare da jawo hankalin kafofin watsa labaru na kasar Sin dama babban kocin kungiyar dan kasar Croatia.

Game da sirrin samun wannan nasara kuwa, Tomic ya bayyana wa 'yan jaridu cewa sirrin shi ne namijin kokari wajen aiki. Ya ce 'yan wasan kungiyar na hada kai da juna, wanda hakan ya haifar da kyakkyawan sakamakon da ake gani. Har way au Tomic ya ce, shi kasan sa ya taba taka leda a baya, don haka ya san abu ne mai wuya ga wata kungiya ta iya lashe wasanni 5 a jere, amma gas hi kungiyarsa ta Baxy ta samu nasara a wasannin ta har guda 21 a jere. Ya ce wannan sakamako ne mai matukar ban sha'awa kwarai.

A daya bangaren kuwa, wannan nasara da kungiyar ta samu ya janyo ma ta matsin lamba duba da cewa ko wace kungiyar na kokarin doke ta a yayin haduwar su, har ma ya zama buri na ko wace kungiya ta zamo ta farko da za ta doke Baxy a wannan kakar wasanni dake daf da karewa. Game da hakan Tomic ya ce, nasarar da kungiyar Guangdong Sunray Cave FC ta samu kan kungiyar ta Baxy, ita ce ta sassauta halin da mambobin kungiyar ke ciki.

A 'yan kwanakin baya an fidda wani sharhi kan shafin yanar gizo na Goal.com, wanda ya haska nasarar da wannan kulaf na Baxy ya samu, sharhin da ya bayyana cewa, Tomic ya shige gaban Marcello Lippi da Sven-Goran Eriksson wajen kwarewar huras da 'yan wasa. Game da hakan Tomic ya ce mai yiwuwa ne marubucin wancan sharhi ya yi la'akari ne da nasarar lashe wasanni 21 a jere da Baxy ya yi karkashin sa, wanda hakan abin a yaba ne, sai dai Tomic ya ce yana matukar girmamawa wadannan mashahuran koci wato Lippi da Eriksson. A daya bangaren kuma kungiyarsa ta Baxy na kokarin shiga gasar China Super League, kuma idan har hakan ta tabbata za ta samu damar karwa da kungiyoyin da Lippi da Eriksson ke jagoranta yanzu haka.

Ya zuwa kakar wasannin bana, Tomic ya kasance babban kocin waje, mafi dadewa a tarihin kungiyar Baxy, kana yana daya daga cikin kocin waje mafiya dadewa a tarihin kungiyoyin dake buga gasar China League. Kasancewar ba abu ne mai sauki babban koci daga waje ya yi aiki a kasar Sin ba, Tomic ya bayyana farin ciki matuka da samun kyakkyawan sakamako irin wanda ya cimma a wa'adin aikin sa. A ganinsa, bambancin hanyoyin nazari tsakanin kasashen gabashin duniya, da na yammacin duniya shi ne tushen samun matsalolin da kocin kasashen waje ke fuskanta yayin da suke yi aiki a kasar Sin.

Har wa yau Tomin ya bayyana cewa, kasar Sin tana da bukatar masu horas da 'yan wasa na ketare su yi aiki matuka, ya na mai farin cikin yadda kungiyar Baxy ta kafa dangantaka mai kyau da shi kansa, kana ta nuna matukar amincewa da shi.

Tomic wanda yanzu haka ke nan kasar Sin tsawon shekaru biyu, kuma ya ce sannu a hankali rayuwarsa ta daidaita a nan birnin Beijing, ya bayyanawa 'yan jarida yadda yake kaunar birnin na Beijing. Kana ya yi fatan ci gaba da yin aiki a birnin na Beijing a shekaru masu zuwa.

Bisa yarjejeniyar sa da kungiyarsa ta Baxy, Tomic na da ragowar shekara daya ta aiki a kungiyar. Koda yake ya ce ana da imanin ci gaba da zama a kungiyar, ko kuma ya bar ta bayan kammala kakar wasanni ta bana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China