in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Arsene Wenger ne dalilin rashin ci gaban Arsenal
2014-09-26 16:44:01 cri

A fagen wasan kwallon kafa, kulof din Arsenal na kasar Birtaniya daya ne daga cikin manyan kulflika masu karfi,wanda kuma ke da tsawon tarihi. Sai dai a shekarun baya, masu sha'awar kwallon kafa na ganin cewa, kungiyar ba ta sheda karfi sosai ba, lamarin da ke sanya masu goyon bayan kungiyar bakin ciki.

Ga misali, a karawa ta farko da aka yi a zagayen rukunai na gasar cin kofin zakarun turai (UEFA Champions League) ta kakar 2014 zuwa ta 2015, kulob din Dortmund ya lashe Arsenal da ci 2 da nema. Wannan wasan ya bayyana ainihin yanayin da Arsenal take ciki, ganin yadda Dortmund ta kai hari gidan Arsenal sau 24 yayin da Arsenal ta kai hari gidan Dortmund sau 4 kawai. Ta haka, ma iya cewa rashin tabuka abin azo-a-gani na kulob din Arsenal ya sa ta rashin samun nasara, musamman ma lokacin da take karawa da wata kungiya mai karfi, wadda ke kokarin neman samun maki a wasa.

A kakar wasa da ta wuce, mun ga yadda Chelsea ta doke Arsenal da ci 6 da ba ko daya, da yadda Liverpool ta yi kaca-kaca da Arsenal da ci 5 da 1, yayin da Manchester City ita ma ta doke Arsenal da ci 6 da 3. Yanzu a gasar cin kofin zakarun turai (UEFA Champions League), Arsenal ta sake shan kashi. Ma iya cewa, kusan kowace kungiya mai karfi za ta iya cin Arsenal ke nan.

Kamar yadda wani mai sharhi kan harkokin wasanni na jaridar The Daily Telegraph ta kasar Birtaniya, Henry Winter, ya yi tsokaci kan wasan da aka yi tsakanin Arsenal da Dotmund, inda ya ce, "Arsenal ba ta da kuzari da jajircewa, kuma ba ta kare gidanta yadda ya kamata ba. A ganina sun yi sa'a ne, da aka ci su kwallaye 2 kawai. Hakika 'yan wasan kungiyar Dotmund masu hazaka da kwazo sun keta masu tsaron bayan Arsenal. Domin 'yan wasan bayan Arsenal malalata ne kwarai, ba su gudu, kana duk lokacin da aka matsa musu lamba, sai su rasa abin yi."

Maganar Winter tana bisa hanya, ganin yadda 'yan wasan Dortmund suka kai hari gidan kungiyar Arsenal har sau 24, yayin da 7 daga cikinsu suka kusan shiga raga. Mun ga yadda Aubameyang ya samu kwallon da mai tsaron gida Weidenfeller ya jefa masa, sa'an nan ya yi gudu ya buga kwallon gidan Arsenal ba zato ba tsammani, sai dai kwallon ta ci karo da turke ta fita.Haka Dotmund ta yi ta kai hari, don haka da kungiyar ta kara lura da damar da ta samu, za ta iya cin Arsenal 4 da banza. Sai dai a nasu bangare, 'yan wasan Arsenal sun kai hari gadin Dortmund sau 4 ne kawai. Kana a cikinsu ban da kwallon da Welbeck ya buga, saura ko kadan ba su yi hadari ga Dortmund ba.

Idan mun dubi wasannin da Arsenal ta buga a baya, za mu san cewa wannan ba shi ne karo na farko da kungiyar ta sha mummunan kashi ba. A kakar wasa ta 2013 zuwa 2014, Arsenal ta sha kashi a karawar da suka yi da mayan kuloflika 3. Kamar yadda Man. City ta lashe Arsenal ci 6 da 3, lamarin da ya zama mummunan kashin da Arsenal ta sha a tarihi. Sa'an nan Liverpool ta sake cin Arsenal 5 da 1, inda aka ci Arsenal kwalle 4 a cikin mintuna 20 da fara wasa. Domin ko a tarihin gasar Premier ma ba a taba ganin irin wannan ruwan kwallaye da aka yi kamar haka ba. Daga bisani karawar da Arsenal ta yi da Chelsea ta kasance wasa na 1000 da Arsenal din ta yi karkashin jagorancin kocin ta Arsene Wenger, amma a wancan wasan kungiyar ta sha kashi sosai, inda Chelsea ta lashe ta da ci 6 da nema!

Tsohon dan wasan kulob din Manchester United, wanda yanzu ke sharhi kan harkokin wasanni, Paul Scholes, ya taba bayyana matsalar Arsenal kamar haka, 'duk lokacin da Arsenal ta kara da wata kungiya mai karfi sosai, ta kan rude, saboda ta kan nuna karaya wajen tinkarar kalubale.

Hakika wannan batun ya kasance wata babbar matsalar da take hana Arsenal samun nasara a wasannin da ta ke yi musamman ma a shekarun baya. Idan ba mu manta ba a zagaye na 3 na gasar Premier ta kakar wasa ta 2011 zuwa ta 2012, Manchester United ta lashe Arsenal da ci 8 da 2, kashin da Arsenal ba ta taba shan irinsa ba shekaru 115 da suka wuce. Haka kuma a kakar wasan da ta gabata, Man. City ta doke Arsenal ci 6 da 3, Liverpool ta lashe ta da ci 5 da 1, Chelsea ta fatattaka ta da ci 6 da banza, Everton ita ma ta zura mata kwallaye 3 da nema. A wadannan wasanni 4 baki daya an zura wa Arsenal kwallaye 20 a raga!

Yayin da 'yan wasan Liverpool suke kai hari cikin sauri da kuzari, Arsenal tana wasan ne kamar ruwa ya ci ta, lamarin da ya sa aka jefa mata kwallaye 4 cikin mintuna 20 da fara wasa. Kana a karawar da Arsenal ta yi da Chelsea, Wenger ya fada tarkon da Mourinho ya dana masa, ganin yadda Mourinho ya yiwa Wenger lakabi da 'sarkin shan kaye' kafin karawar, abin da ya sanya Wenger ya canza wani salon buga wasa na 4-1-4-1 don nuna cewa kungiyarsa ta iya kai hari. Amma ga shi Eto'o tsohon dan wasan Chelsea da Andre Schurrle, da Eden Hazard na kungiyar Chelsea suka dinga kara kwallo a mintuna 17 na farkon rabin lokaci.

Amma me ya sa Arsenal ta kasa tabuka komai yayin da take karawa da sauran manyan kungiyoyi? Game da wannan, manazarta kan harkokin wasanni na ganin cewa, babban kocin kungiyar Wenger shi ke da laifi.

Hakika akwai wasu ra'ayoyi guda biyu game da Arsene Wenger, wasu na ganin cewa, Wenger ya yi shekaru 18 yana jagorantar kungiyar Arsenal, wadda ta taba samun nasarori da yawa a tsawon wannan lokaci, saboda haka ya kamata a girmama kocin, yayin da wasu ke kallonsa a matsayin dalilan da suka haddasa koma bayan kungiyar ta Arsenal, don haka ya kamata a kore shi.

A matsayin sa na mutum, ba za a rasa masu kaunarsa da wadanda ba sa kaunar sa ba, amma idan aka binciki halayyar Wenger, za mu ga cewa,shi kansa ba mutun ne mai jajircewa ba, abin da ka iya yin tasiri kan 'yan wasansa. Don haka, mai sharhi kan harkokin wasanni Gary Lineker ya taba yin hasashe a shekaru 10 da suka wuce, cewa Wenger yana amfani da tsohuwar fasaha, kuma bai mai da hankali kan dabarar tsaron gida sosai ba, don haka wannan zai iya sanya kungiyar Arsenal ta rika shan kashi a wasanninta.

Hasashen da Lineker ya yi yanzu ya zama gaskiya, ganin yadda Wenger ya kasa canza tsohuwar fasaharsa, kuma ya fi mai da hankali kan kai hari maimakon tsaron gida. Ga misali, Wenger ya ware makudan kudi don sayo kwararrun 'yan wasan gaba, amma bai shigo da isassun 'yan wasan baya ba.

Yanzu a kungiyar Arsenal akwai 'yan wasan gaba 20, yayin da 'yan wasan baya 6 ne kawai. Sai dai sakamakon raunin da suka ji, wasu kwararrun 'yan wasan bayan kungiyar kamarsu Mathieu Debuchy da Nacho Monreal ba sa buga wasanni a halin yanzu. Abin da ya tilasta Wenger yin amfani da dan wasa mai shekaru 19 a duniya Bellerin, wanda aka kwace kwallo daga wajensa har sau 21.

Bisa la'akari da yanayin da kungiyar Arsenal take ciki ya sa ake tambaya cewa, ko kulob din Arsenal ba shi da isasshen kudi ne don kara sayen wasu fitattun 'yan wasan baya? Amma hakika batun kudi ba shi ne dalili ba, ganin yadda Wenger ya iya ware Euro miliyan 50 don sayo Mesut Ozil, da yadda ya kashe fam miliyan 34 don sayo Alexis Sanchez daga Barcelona. Sa'an nan ya sake ware fam miliyan 16 don sayen Danny Welbeck.

Yawan fitattun 'yan wasan gaba da na tsakiya da Wenger ya ke da su ya sa yanzu ya kasa yanke shawarar inda zai saka su don su nuna kwarewarsu. Ga misali Ozil kwararren dan wasa ne da aka sayo da tsada, amma sai ya sanya shi yana buga wasan gefe, don baiwa sauran fitattun 'yan wasa kamarsu Arteta, Ramsey da Wilshere dama. Dalilin haka, a wasan da Arsenal ta yi da Dortmund, Ozil kusan ba shi da amfani ko kadan, abin da ya sanya kafofin watsa labaru suka yi ta sukar Ozil, amma Wenger ne babban mai laifi, domin shi ne bai sanya Ozil a wurin da ya dace ba.

A wannan shekara, wasu 'yan wasan tsakiya kamar su Vermaelen, Djourou da Mique sun bar kungiyar Arsenal, wannan zai sa mutane su fahimci cewa ya kamata a sayo wasu 'yan wasan tsakiya da na baya, amma Wenger ya ki yin wani abu a wannan fanni.

A sa'i daya kuma, sauran manyan kuloflika sun sayo tare da ajiye 'yan wasan baya da dama. Ga misali, Man. City ta ki sayar da Yaya Ture, Fernandinho, kana ta kara sayo Fernando Reges a kakar sayar da 'yan wasa ta wannan lokaci. Yayin da a nata bangare Chelsea ta rike Matic, Fabregas, Ramires, da Mikel John Obi. A bangaren Liverpool kuma tana da Gerrard, Henderson da Joe Allen. Ita kuma Manchester United ta sayi Daley Blind yayin da aka bude kasuwar sayar da 'yan wasan, amma shi Wenger bai yi kome ba don kara karfin 'yan wasan bayan kungiyarsa ba.

Idan ba a manta ba Wenger ya taba sayan wasu fitattun 'yan wasa, wadanda suka sanya Arsenal zama zakarar kuloflikan gasar Premier. A lokacin Wenger yana da Lehmann wanda ke tsaron gidan kungiyar Arsenal, da Sol Campbell da Kolo Toure, 'yan wasan tsakiya. Sa'an nan a gefuna 2 akwai Laureano da Ashley Coke, yayin da a tsakiya akwai Vieira da Silva. Amma bayan da wadannan 'yan wasan suka bar Arsenal, Wenger ya kasa samun 'yan wasan da za su maye gurbinsu domin su kara karfin tsaron bayan kungiyar ta Arsenal.

A halin yanzu 'yan wasan bayan Arsenal da dama kamar su Senderos, Vermaelen da Djourou suna fama da raunuka daban daban, amma duk da haka Wenger ya ki mai da cikakken hankali kan shigo da wasu kwararrun 'yan wasan baya, maimakon haka ya fi mai da hankali kan amfani da 'yan wasan gaba.

Sa'an nan a fannin fasahar jagorantar kungiyar a yayin wasa, Wenger yana da taurin kai sosai, ba ya so ya canza salon wasan da ya ke amfani da shi shekaru 10 da suka wuce. Hakika idan mun koma kakar wasa ta 2003 zuwa 2004, za mu ga cewa Arsenal ta taka rawar gani sosai, inda bisa salon wasa na 'yan wasa 4 a gaba 4 a tsakiya 2 a baya wato 4-4-2 da Wenger ke amfani da shi, kungiyar tana iya doke kowace kungiya a gasar Premier. Sai dai yanzu, yanayi ya canza, kungiyoyi kamarsu Man. City da Chelsea sun taso, yayin da ita kuma Arsenal karfinta ya ragu sosai. Shi kuma Wenger ya ci gaba da amfani da salon kai hari a karawar da kungiyarsa ta yi tare da wasu manyan kungiyoyi, abin da ya sanya Arsenal ta kasa samun nasara.

Ta la'akari da wannan yanayi da kungiyar Arsenal take ciki, ya kamata babban kocin kungiyar Arsene Wenger ya sauya tunaninsa don warware halin da kungiyar take fuskanta. Amma idan Wenger ya ci gaba da nuna tauri kai tare da kin daukar matakai na kwaskwarima to, ana iya hasashen cewa, nan ba da dadewa ba Arsenal za ta iya korar sa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China