in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin mika kayayyakin taimako na Sin ga Najeriya domin yaki da cutar Ebola
2014-11-18 10:26:42 cri

Yayin bikin, jakada Gu Xiaojie ya bayyana cewa, kayayyakin da kasar Sin ta baiwa Najeriya a wannan karo, wadanda kimar su ta kai kudin Sin Yuan miliyan 10, sun kasance wani bangare na daukacin ayyukan da gwamnatin kasar Sin ta gudanar, domin taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da cutar Ebola.

Har wa yau Gu Xiaojie ya ce, a nan gaba kasar Sin za ta kara yin hadin gwiwa da Najeriya, da sauran kasashen Afirka a fannonin kiwon lafiya, da yaki da cututtuka masu yaduwa, bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afirka.

A nasa bangare, minista Alhassan ya jinjinawa gwamnatin kasar Sin, bisa gudummawar da take baiwa Najeriya wajen yaki da yaduwar cutar Ebola a wannan lokaci. Kana ya ce, kayayyakin da gwamnatin kasar Sin ta samar za su taimakawa kasar, wajen ci gaba da dakile bullar cutar Ebola, da kara samar da taimako ga sauran kasashen dake makwabtaka da kasar a wannan fanni. (Zainab)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China