Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a Litinin din nan ta yi maraba da shirin da kasar Sin ta sanar na gina asibiti mai gidaje 100 a kasar Liberiya. Madam Nkosazana Dlamini-Zuma, shugaban kwamitin kungiyar ta yi wannan maraba cikin wata sanarwa da cibiyar kungiyar ta fitar inda ta ce, wannan zai kara yawan kayayyakin ba da agajin rage yaduwar wannan annoba da kasashen Amurka, Faransa, Britaniya da sauran kasashen dake ba da gudunmuwa suka yi a Guinea, Saliyo da kuma Liberiya wadanda rashin ababen kayayyakin ya kara kawo jinkiri da mai da aiki baya da ake yin a dakile cutar.
Wannan sanarwar baya bayan nan ta biyo kayan agajin da tuni kasar ta Sin ta riga ta samar domin ba da gudunmuwar dakile annobar ta Ebola. Wadanda suka hada da kayayyakin aikin asibiti, ma'aikatan jinya, da rigunan ba da kariya. Sauran sun hada da samar da taimakon abinci, kudi ga kasashe uku da cutar ta fi kamari, sa'an nan kuma ta tura likitocinta zuwa kasashe.
A kan wadanan har ila yau kasar ta Sin ta riga ta ba da gudumuwar kudi har dalar Amurka miliyan biyu ga kungiyar AU domin taimake ta wajen nata ayyukan dakile cutar, da kuma ita kanta hukumar kiwon lafiya ta WHO, da ma ofishin MDD mai kula da shirin ko ta kwana a kan barkewar cutar ta Ebola. (Fatimah)