Dangane da jawabin da shugaba Obama ya bayar, jiya Asabar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya amsa wasu tambayoyi game da hakan. Mr. Qin ya ce, cikin jawabinsa, shugaba Obama ya jaddada cewa, kasar Amurka na maraba da gano bunkasuwar kasar Sin cikin yanayin zaman lafiya da na zaman karko, don gane haka, kasar Sin na fatan yin hadin gwiwa tare da kasar Amurka wajen karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu domin warware da yin rigakafi kan sabanin dake tsakaninsu, bisa ra'ayoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a birnin Beijing. Kana ya kamata kasashen biyu su gudanar da ka'idojin mutunta juna da kuma cimma moriyar juna yadda ya kamata, ta yadda za a iya ciyar da gina sabuwar dangantakar manyan kasashe dake tsakanin Sin da Amurka gaba, da kuma samu sakamako mai gamsarwa. Wannan ba kawai ya dace da moriyar jama'ar kasashen biyu ba, zai kuma inganta yanayin zaman lafiya, zaman karko da kuma bunkasuwar duk fadin yankin Asia-Pacific, har ma da na kasa da kasa. (Maryam)