in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai halarci taron shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS karo na 6
2014-07-07 14:41:07 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya sanar a ranar 7 ga wata cewa, bisa gayyatar da shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS karo na 6 da za a yi daga ranar 15 zuwa 16 ga wata a kasar Brazil.

Bisa gayyatar da shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, shugabar kasar Argentina Cristina Fernandez de Kichner, shugaban Venezuela Nicolas Maduro, shugaban kasar Cuba Raul Castro suka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara a kasashen hudu tun daga ranar 17 zuwa 23 ga wata, kana zai halarci ganawa tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen yankin Latin Amurka da Caribbean yayin da yake ziyara a kasar ta Brazil. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China