in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping zai halarci taron kungiyar BRICS a kasar Brazil
2014-07-13 16:26:43 cri
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing zuwa Brazil, domin halartar taron kasashe mambobin kungiyar BRICS karo na shida da za a yi a kasar.

Kaza lika rahotanni sun ce baya ga taron na BRICKS, shugaba Xi zai gudanar da ziyarar aiki a kasashen Brazil, Argentina, Venezuela, da kuma Cuba, bisa gayyatar da jagororin kasashen suka yi masa.

Bugu da kari, a yayin ziyararsa a kasar Brazil, ana sa ran shugaba Xi zai halarci taron tattaunawa, tsakanin shugabannin kasar Sin da na kasashen Latin American da Caribbean. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China