Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin a taron shugabannin kasashen BRICS karo na shida da aka gudana a birnin Fortaleza na kasar Brazil.
A cikin jawabin nasa mai taken "Sabon mafari, sabon buri da sabon karfi", Mr. Xi ya yi tsokaci game da fasahohin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, inda ya gabatar da shawara kan alkiblar da za a bi nan gaba. A cewarsa kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasashen BRICS, da ba da gudunmawarta wajen kiyaye zaman lafiya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa a dukkanin fannoni.
Dadin dadawa, Mr Xi ya nuni da cewa kamata ya yi kasashen BRICS su rungumi ka'idar bude kofa, da hakuri da juna, da hadin kai, da bunkasa cimma moriyar juna, domin kara bunkasuwar dangantakar abokantaka a dukkan sassan bisa fasahohi da aka cimma a cikin shekaru biyar da suka gabata.
Bugu da kari shugaba Xi ya ce da farko kamata ya yi a bunkasa tattalin arziki na bola jari, ta yadda za a hada bunkasuwar tattalin arziki da aikin kiyaye muhalli tare. Na biyu akwai batun tsaya tsayin daka wajen hadin gwiwa a dukkanin fannoni tsakanin kasashe mambobi, da kafa wata kasuwa bai daya ta cinikayya da zuba jari, tare da daukar wasu matakai da suka dace domin samun nasarar hada-hadar kudi da sauransu. Na uku a cewar shugaban na kasar Sin yana da kyau a shimfida kyakkyawan yanayi na kyautata yanayin tattalin arzikin duniya, da tabbatar da ikon samar da wakilci, da ikon fadin albarkacin baki ga kasashe masu tasowa.
Abu na karshe kuma shi ne tsayawa tsayin daka wajen daga matsayin kasashen BRICS na yada kyakkyawan tunaninsu, da gabatar da tsare-tsarensu cikin harkokin duniya, da kiyaye daidaito da adalci, baya ga kara kwazo wajen bunkasa dangantakar hadin kai tsakanin kasashen duniya. (Amina)