in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai halarci taron koli na shugabannin membobin kungiyar APEC kan batun masana'antu da cinikayya
2014-10-30 14:43:44 cri
Kungiyar sa kaimi ga bunkasuwar ciniki ta kasar Sin ta bayyana a ranar 30 ga wata a nan birnin Beijing cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron koli na shugabannin membobin kungiyar APEC kan batun masana'antu da cinikayya tare da gabatar da jawabi. Mataimakin shugaban kungiyar kuma mataimakin shugaban kwamitin shirya taron kolin Yu Ping, ya sanar da hakan a gun taron manema labaru game da taron.

Yu Ping ya yi bayani cewa, za a gudanar da taron koli na shugabannin membobin kungiyar APEC kan batun masana'antu da cinikayyar ne tun daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Nuwanbar dake tafe a nan birnin Beijing. Ya zuwa yanzu, shugabannin kasashen Amurka, New Zealand, Chile, Peru, Indonesia, yankin Hongkong na kasar Sin da sauran kasashe da yankuna sun tabbatar da aniyarsu ta halartar taron kolin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China