UNICEF za ta kara yawan ma'aikatanta a kasashen yammacin Afirka don taimakawa wajen yaki da cutar Ebola
Jami'in asusun tallafawa yara na MDD UNICEF kan cutar Ebola Peter Salama ya bayyana a ranar 3 ga wata cewa, a sakamakon yadda cutar ta yi mummanan tasiri ga kananan yara a kasashen yammacin Afirka masu fama da cutar Ebola, asusun zai kara yawan ma'aikatansa a kasashen daga 300 zuwa 600 don taimaka musu wajen yaki da cutar Ebola.
Salama ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a cibiyar MDD dake birnin New York a wannan rana cewa, asusun zai kuma taimaka wajen tsugunar da yara marayu kimanin 4000 da suka rasa iyayensu sakamakon cutar ta Ebola. (Zainab)