A ran 5 ga watan, yayin da Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin yake ganawa da takwaransa na kasar Kwadivwa Mr. Charles Koffi Diby wanda yake ziyarar aiki a nan kasar Sin, a madadin gwamnatin kasar Kwadivwa ya nuna godiya sosai ga gwamnatin kasar Sin sabo da samar wa kasashen yammacin Afirka, ciki har da kasar Kwadivwa taimakon kudi da kayayyakin jin kai domin shawo kan cutar Ebola. Mr. Diby ya jaddada cewa, wannan taimako da kasar Sin ta bayar ya kara karfin rigakafin yaduwar cutar da imanin jama'a da kasashen Afirka wajen shawo kan cutar. Wani muhimmin dalilin da ya sa har yanzu ba a samu bullar annobar a kasar Kwadivwa ba shi ne ta samu taimakon da kasar Sin ta bayar cikin sahihanci, kuma cikin hanzari.
A nasa bangaren, Mr. Wang Yi ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka tamkar 'yan uwa ne wadanda suke fadi tashin wahala tare, kuma suke fama da matsaloli tare. Lokacin da 'yan uwa na kasashen Afirka suke fama da annobar Ebola, gwamnati da jama'ar kasar Sin ma ba su ji dadi ba, wannan ya sa dole ta bayar da taimako. Ko da yake kasar Sin kasa ce mai tasowa, amma tana iya nata kokarin gwargwadon karfinta. (Sanusi Chen)