Wadannan kayayyakin dai sun hada da hular kwano ta kariya, da rigar kariya, da tantuna na killace masu dauke da cutar da sauransu, wadanda cibiyar nazarin kayayyakin kiwon lafiya dake kwalejin kimiyyar kiwon lafiya ta rundunar sojojin kasar Sin ta yi bincike tare da samar da su, kuma a kwanan baya aka yi amfani da nau'in wadannan kayayyaki a yankunan da cutar ta Ebola ta bulla a baya, musamman kasashen Saliyo da Mali.
Rahotanni dai sun bayyana yadda wadannan kaya suka bada kariya ga masu aikin bincike da likitocin Sin dake kasashen.
Wadannan kaya dai sun zamo cikin muhimman abubuwa da wannan kwaleji ta samar, domin kandagarkin yaduwar cutar ta Ebola.
Da yake karin haske game da hakan, daya daga kwararru a wannan fage Qi Jiancheng, ya ce sun yi nazari kan kayayyakin kariyar, sun kuma yi amanna da cewa kayan za su biya bukatun da ake da su na kare likitoci daga cutar ta Ebola yayin da suke gudanar da aiki, kana ingancinsu ya yi daidai ko ma ya zarce na irin wadanda ragowar kasashen waje ke kerawa. (Zainab)