Za'a saka sanarwar yaki da cin hanci a takardun bayan taron kungiyar yin hadin gwiwa a yankin Asiya da tekun Pacific ta fuskar tattalin arziki wato APEC da za a gudana a nan birning Beijing, in ji wani jami'in kungiyar APEC.
Alan Bollard, direktan zartaswa na sakatariyar kungiyar APEC ya ce, sanarwar Beijing da za a bayar game da cin hanci ba shugabannin kasar Sin kadai suka ba da shawarar bayarwa ba, har ma da Amurka.
Mr. Bollard ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai, inda ya kara da cewa, sanarwar za ta haifar da kafa wata kungiya wadda za ta samo hukumomin da za su sa ido a yankin APEC, za ta kuma ba su damar isar da sako a kan ko wane abu ya taso ga saura.
Ya ce, wannan yana da muhimmanci wajen bin diddigin abubuwan dake faruwa a yankin a kuma bi bahasi har a kwato kaddarori idan har an kai su wani wuri ba bisa doka ba.(Fatimah)