in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayar da sanarwar hadin kai ta taron ministocin kudi na APEC karo na 21
2014-10-23 16:16:21 cri

A jiya ne aka rufe taron ministocin kudi na APEC karo na 21 a nan birnin Beijing, inda a karshen ganawar aka bayar da hadaddiyar sanarwa game da batutuwa hudu da aka tattauna a gun taron. A cikin sanarwar, bangarori daban daban masu halartar taron sun yi alkawarin kara yin kwaskwarima kan tsare-tsare da daukar matakai don warware matsalolin da aka fuskanta yayin da ake raya tattalin arziki da kuma gano sabbin hanyoyin sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki.

A gun taron ministocin kudi na kwana daya, ministocin kudi daga mambobin kungiyar ta APEC sun tattauna kan halin tattalin arziki da duniya da yankin Asiya da tekun Pasific ke ciki, da yadda za a hada gwiwa kan zuba jari ga ayyukan more rayuwa, da manufofin kudi dake shafar kyautata tsarin tattalin arziki, kana da yadda za a mara baya ga bunkasuwar tattalin arzikin shiyya-shiyya ta hanyar hada-hadar kudi da dai sauransu, sun kuma cimma daidaito da samun kyakkyawan sakamako kan wadannan batutuwa.

Ministan kudi na kasar Sin Lou Jiwei ya yi bayani cewa, zuba jari ga ayyukan more rayuwa shi ne batun da aka fi mayar da hankali a kai a gun taron na wannan karo. Ministocin kudi kungiyar da suka halarci taron sun bada shawarar yin amfani da hanyar tattara kudi wajen jawo jari da kuma kudi daga al'ummar kasa don warware matsalar karancin kudi a bangaren ayyukan more rayuwa da yankin Asiya da tekun Pasific ke fuskanta a halin yanzu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China