A cikin jawabin da ya bayar, Zhang Gaoli ya bayyana cewa, wannan taron ministocin kudi wani muhimmin taro ne na kungiyar APEC da ake da shirin gudanarwa a kasar Sin a bana, inda za a tattauna kan halin tattalin arziki da duniya da yankin Asiya da tekun Pasific ke ciki, da yadda za a hada gwiwa kan zuba jari ga ayyukan more rayuwa, da manufofin kudi dake shafar kyautata tsarin tattalin arziki, kana da yadda za a mara baya ga bunkasuwar tattalin arzikin shiyya-shiyya ta hanyar hada-hadar kudi da dai sauransu, wadanda ke da babbar ma'ana a zamanin yau.
Ban da wannan kuma, Zhang Gaoli ya ce, kasar Sin kasa ce a yankin Asiya da tekun Pasific, ba a iya rabawa bunkasuwarta da ci gaban yankin. Kasar Sin za ta yi kwaskwarima da kirkire-kirkire don sa kaimi ga bunkasuwata a fannonin kimiyya da fasaha, tsare-tsare, ayyukan gudanarwa, da kuma salon cinikayyya, a kokarin karfafa zukatan kamfanoni da jama'a wajen raya ayyukansu, ta yadda za a iya samun dauwamammen ci gaban tattalin arzikinta, har ma a kasance a kan gaba. Haka zalika kuma, kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje, da kyautata yanayin cinikayya, domin jawo kamfanonin kasashen waje da su zuba jari a kasar Sin. Bunkasuwar kasar Sin, a cewar Mr. Zhang, za ta kara samar da damar ci gaba ga yankin Asiya da tekun Pasific har ma duk duniya baki daya. (Zainab)