A yau Talata da yamma ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugabannin kungiyoyin da za su halarci taron ministocin kudi da tattalin azrki na kungiyar hadin kan nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific wato APEC karo na 21, wanda za a bude gobe Laraba 22 ga wata a nan Beijing.
A yayin ganawar, mista Li ya ce, ana nuna karfin hali kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, yayin da ake yin taka tsan-tsan wajen tinkarar kalubaloli da Sin take fuskanta. Kasar Sin za ta yi namijin kokari wajen cimma muhimman manufofin da aka tsara a bana.
Mista Li ya kara da cewa, kasar Sin na himmantuwa wajen kara azama kan raya tattalin arziki da yin hadin gwiwa a nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific,kana tana son hada kai da mambobin kungiyar APEC wajen sa kaimi ga samun kyakkyawan ci-gaban tattalin arziki mai dorewa kuma cikin daidaito a duniya da ma yankin da kungiyar take ciki. Har wa yau kasar Sin na fatan taron ministocin kudi na APEC zai yi kokarin lalubo bakin zauren yin gyare-gyare kan yadda za a raya tattalin arzikin nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific a nan gaba, da sa kaimi kan yin hadin gwiwar a-zo-a-gani a yankin ta fuskar tattalin arziki, a kokarin kyautata hadin gwiwar APEC yadda ya kamata.
Mr.Joe Hockey, ministan kudi na kasar Australia da sauran wadanda suka halarci ganawar sun nuna cewa, kasar Sin ta samu kyakkyawan bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa. Ci-gaban tattalin arzikin Sin na amfanawa nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific, da ma duniya baki daya.Don haka suna son yin kokari tare da kasar Sin wajen tabbatar da ganin an gudanar da taron APEC cikin nasara. (Tasallah)