in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron karshe na manyan jami'ai gabanin bude taron koli na kungiyar APEC
2014-11-05 15:10:16 cri
An gudanar da taron karshe na manyan jami'ai gabanin bude taron koli na kungiyar APEC na shekarar 2014 a Larabar nan 5 ga wata a birnin Beijing, matakin da ya bude makon taruruka na shugabannin membobin kungiyar ta APEC na bana.

Za a dai shafe kwanaki biyu ana gudanar da taron manyan jami'an, wanda ya zamo tubali ga kwarya-kwaryan taron shugabannin mambobin kungiyar APEC karo na 22 da za a gudanar tun daga ranar 10 zuwa 11 ga wata.

Shugaban taron manyan jami'an kungiyar ta APEC, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong ne ya shugabanci taron tare da yin jawabi.

Taron manyan jami'an a wannan karo dai shi ne taron farko a makon taruruka na shugabannin membobin kungiyar APEC. Bayan taron za a gudanar da taron ministocin harkokin waje, da na ciniki, na kungiyar ta APEC, da taron koli na shugabannin masana'antu da ciniki na APEC da sauran taruruka.

A matsayin taro mafi muhimmanci, babban taron shugabannin membobin kungiyar ta APEC karo na 22 zai gudana ne tun daga 10 zuwa 11 ga wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China