in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta share fagen taron APEC, in ji ministan harkokin wajen kasar
2014-10-29 20:44:12 cri
A yau Laraba 29 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta Sin ta shirya taron dandalin tattaunawa karo na 10 a birnin Beijing, inda ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi jawabi mai taken "Sin ta riga ta share fagen taron APEC".

Jakadun kasashen waje a Sin, da wakilan kungiyoyin duniya, da wakilan sassan masana'antu, da masanan kasar da nakasashen waje, da manema labarai na gida da na waje kimanin 300 suka halarci dandalin.

A cikin jawabinsa, Wang Yi ya bayyana cewa, za a kira kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashen kungiyar APEC karo na 22 a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasashen kungiyar APEC za su yi shawarwari kan makomar kungiyar da shirin bunkasa yankin Asiya da tekun Pasifik.

Bana ta cika shekaru 25 da kafuwar kungiyar ta APEC, a don haka bangarori daban daban suna sanya ran yankin Asiya da tekun Pasifik zai ba da jagoranci wajen farfado da tattalin arzikin duniya. Haka kuma ana fatan Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen raya kungiyar APEC da yankin Asiya da tekun Pasifik baki daya. Ministan harkokin wajen kasar yace a lokacin taron Sin za ta bayyana ra'ayinta, tare da fitar da shirin kasar, a kokarin ba da gudummawarta yadda ya kamata.

Bayan haka, Wang Yi ya kara da cewa, za a kaddamar da taron APEC nan ba da dadewa ba kuma Sin a shirye take kuma Beijing ma a shirye take!(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China