Yayin taron da aka saba yi, kakakin babban magatakardan MDD Stephane Dujarric ya gabatar da wata sanarwar, inda ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, shekaru 15 ke nan, tun bayan gudanar da bincike kan aikin kiyaye zaman lafiyar a karo na farko, don haka aikin kiyaye zaman lafiyar a yanzu na fuskantar karin matsaloli. Baya ga fama da hare-haren da sojojin kiyaye zaman lafiya ke fuskanta.
Hakan a cewar sa ne ya haifar da bukatar gudanar da bincike kan matakan da MDD za ta dauka wajen inganta aikin kiyaye zaman lafiyar da kuma ba da taimako ga kasashen da hare-haren ke shafa yadda ya kamata, da kuma tabbatar da karfin sojojin kiyaye zaman lafiya da na tawagogin siyasa cikin yanayin kasa da kasa mai canzawa. (Maryam)