Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya ce, zaman lafiya ginshiki ne na bunkasa zamantakewar al'ummar duniya, baya ga kasancewar hakan jigon kaucewa tashe-tashen hankula.
Mr. Ban wanda ya bayyana hakan yayin wani babban taron tattaunawa kan wanzar da zaman lafiya, ya kara da cewa, zaman lafiya ne kadai ke iya share fagen habaka ilimi, da kiwon lafiya da damar samarwa al'ummar duniya ababen more rayuwa, musamman ma ga mata da kananan yara.
Kaza lika Mr. Ban ya ce, a wannan lokaci da rigingimu da tashe-tashen hankula, tare da ayyukan ta'addanci ke yaduwa tamkar wutar daji, kamata ya yi a sanya dan-ba na inganta dabi'ar shiga tsakani, da warware rigingimu, tare da wanzar da zaman lafiya a dukkanin fadin duniya. (Saminu)