Cikin jawabinsa, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, zaman lafiya da tsaro su ne manyan tushen ci gaban zaman takewar al'umma da kuma samun dauwamammen ci gaban kasa da kasa, hanyar zaman lafiya ita ce hanyar da za a bi ta dindindin, ya kuma yi kira da a yi tunani kan wannan batu, domin fahimtar da ma'anar zaman lafiya ga dukkanin jama'ar kasa da kasa, ta yadda za a iya kiyaye wannan ma'ana yadda ya kamata cikin zukatanmu da kuma hankulanmu.
Haka kuma, cikin shekaru da dama da suka gabata, kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da MDD suna ci gaba da kokartawa wajen ba da gudunmawa kan kiyaye zaman lafiya da zaman karko na kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Amma a halin yanzu, ana ci gaba da gamuwa da hare-hare cikin wasu kasashe, shi ya sa kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa ya kasance wani muhimmin aiki mai nauyi kuma na dogon lokaci gare mu. (Maryam)