Yayin taron wanda aka gudanar a nan birnin Beijing, shugaba Xi ya gabatar da wani jawabi mai taken "ci gaba da bin manufar zama tare cikin lumana, da sa kaimi ga kafa sabuwar dangantaka tsakanin kasashen duniya a sabon zamani". Jawabin da ya ja hankalin masharhanta na manyan kafofin watsa labaran kasa da kasa.
A sharhinta mai lakabin "kasar Sin na cewa ba ta da nufin mulkin danniya ga yankinta", kafar watsa labarun "The Associated Press" ta kasar Amurka, ta yi tsokaci game da maganar shugaba Xi ta manufar kasar Sin kan batun tsayawa tsayin daka wajen kauracewa tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen ketare, da kaucewa gudanar da mulkin danniya a duniya, manufar da ya ce babu wata kasa da za ta sanya ta sauyawa.
Kaza lika shi ma kamfanin dillancin labaru na Reuters dake Birtaniya, ya rawaito shugaban kasar ta Sin na cewa, kasarsa za ta ci gaba da neman bunkasuwa cikin lumana, tare da jaddada rashin amincewarta, da manufar kasashe masu karfi, su mulki masu rauni ta hanyar danniya, manufar da a cewar shugaba Xi, ba za ta dace da kudurorin kasar Sin ba. (Maryam)