Sharhin da wannan mujalla ta buga ya nuna cewa, kasar Sin tana kunshe da kabilu 56, wadanda kuma ke bada gudummawa ga kyakkyawar nasara da ci gaban kasar.
Kaza lika ya bayyana yanayin musamman na gurguzu da kasar Sin ke bi, a matsayin tushen samun ci gaban jama'ar kasar Sin, da kuma moriya ta bai daya ga daukacin kabilun kasar. Kana wannan ce hanyar da kasar ke bi wajen samun wadata, da ci gaba, da kuma kyautatuwar rayuwar jama'a.
Don haka ne mujallar ta bayyana daukar matakan jajircewa, wajen bunkasa kasar Sin bisa halayen musamman na gurguzu, ta yadda za a kai ga samun wadata da ci gaba a kasar, tare kuma da samun kyakkyawar makoma ga jihar Xinjiang. (Zainab)