in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An murkushe kungiyoyin ta'addanci 32 a jihar Xinjiang
2014-06-23 15:50:43 cri
Ofishin watsa labaru na jihar Xinjiang ta Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta ya bayyana a gun taron manema labaru a ranar 23 ga wata cewa, tun lokacin da aka fara aiwatar da aikin yaki da ta'addanci a jihar a ranar 23 ga watan Mayu, 'yan sanda na jihar sun murkushe kungiyoyin ta'addanci 32, kana kotun jihar ta yanke hukunci ga mutane 315 membobin kungiyoyin.

Mataimakin shugaban ofishin 'yan sanda na jihar Xinjiang Wang Qianrong ya bayyana a gun taron manema labarun cewa, bisa kungiyoyin ta'addanci da suka murkushe, hakan ya nuna cewa, ayyukan ta'addanci suna da alama, na farko shi ne yawancin 'yan ta'adda suna bin tsattsauran ra'ayin addini, abin da ke sanya su tada rikici. Na biyu kuwa masu ta'addanci ba sa zaune a wuri daya domin su hadu su tsara, shirya da aiwatar da ayyukan ta'addanci. Kuma na uku shi ne ayyukan ta'addanci da suka yi suna da tsanani, duk wanda ya kawo cikas ga ayyukansu ba zai ji dadi ba, ba tare da yin la'akari da bambancin jinsi, shekaru, kabila da addini ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China