in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tura ma'aikatan sa kai 250 a kasashen dake fama da Ebola
2014-10-24 10:23:19 cri

Kasar Najeriya ta kammala aikin aiwatar da tsare-tsarenta domin tura rukunin farko na ma'aikatan sa kai 250 a wasu kasashen yammacin Afrika dake fama da cutar Ebola, in ji wani babban jami'i a ranar Alhamis. Wadannan ma'aikatan sa kai sun fito daga wata tawagar da gwamnatin Najeriya ta jima da ya yi rajistanta a matsayin tawagar da za ta shiga cikin tawagar kasa da kasa da za'a tura domin taimakawa kasashe daban daban yaki da wannan annoba, in ji jami'in sa ido na ma'aikatar kiwon lafiya, Khaliru Alhassan a cikin wata hira tare da manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ma'aikatan sa kan sun samu horo sosai kan yadda ake kulawa da masu kamu da cutar Ebola mafi tsanani da sauran ayyukan dake bukatar kwarewa wajen hana yaduwar Ebola a shiyyar, in ji jami'in. Haka kuma m'aikatan, an horar da su da tattara su yadda ya kamata, kuma za su samu taimako kan wannan aiki nasu daga sauran kwararru da abokan huldar kasa da kasa suka samar, in ji mista Alhassan.

Najeriya ta rike wani rukuni na daban na ma'aikatan sa kai 250 da za'a iyar tura su cikin kasa nan take idan wata matsala ta bullo. Tsaro da lafiyar jikin wadannan ma'aikatan sa kai na da muhimmancin gaske ga gwamnatin Najeriya da kuma abokan huldar ci gaba a cikin tsarin dangantakar bangarorin masu ruwa da tsaki domin murkushe wannan cuta a cikin kasashen yammacin Afrika, in ji mista Alhassan tare da bayyana cewa, Najeriya ta kafa wata cibiyar ayyakun gaggawa ta kasa a birnin Abuja bisa tsarin da alkawarin da gwamnatin kasar ta dauka na kara karfafa matsayinta na kasar da babu cutar Ebola. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China