in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara taron APEC a Bali, kasar Indonesia
2013-10-06 16:36:28 cri
Shugabannin kungiyar hadin kan tattalin arzikin Asiya da yankin Pasific, manyan jami'an kungiyar fiye da 1,200 daga kasashen duniya sun hallara a babban zauren taro na kasa da kasa dake Nusa Dua Bali a kasar Indonesia a ranar Lahadin nan 6 ga wata domin share fagen babban taron shugabannin kasashen APEC , in ji Wisnu Wardhana shugaban taron.

Wisnu Wardhana da yake bayani game da taron ya ce tangal tangal din tattalin arziki na duniya da rashin tabbas game da makomarsa ya nuna yadda taron ya damu da yanayin kasuwannin duniya.

A jawabinsa wajen bude taron Shugaban kasar Indonesiya Susilo Bambang Yudhoyono ya ce cibiyoyi masu zaman kansu suna da tasiri ga ci gaban tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi.

Ya ce taron manyan jami'an da shugabanin na APEC wani dama ne na nuna hanyoyin ci gaban da za'a samu a bangaren cibiyoyi masu zaman kansu a yankin, don haka ya lura da cewa saurin yaduwar kasuwanci ya canza karnin tattalin arziki na 21 da ake ciki zuwa wani mataki mai alfanu.

Shugaban ya yi nuni da cewa gwamnati za ta kasance mai muhimmanci wajen tsara shirye shiryen tattalin arzikin kasa, sai dai in babu taimakon cibiyoyi masu zaman kansu ba za'a iya samar da ayyukan yi ba. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China