in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe mambobin APEC suna taro a kan inganta ci gaba da hadin kan yankin
2013-10-07 17:14:44 cri
A ranar Litinin din nan 7 ga wata a Bali na kasar Indonesiya, aka bude babban taro na shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kan tattalin arzikin Asiya da yankin Pasific APEC, da zummar tattauna ci gaba da kuma hadin kan yankin zuwa wani babban matsayi.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da sauran shugabannin kasashe mambobin kungiyar suna halartar taron wanda shi ne karo na 21, kuma na farko da Shugaba Xi ya halarta tun darewarsa karagar mulkin kasar Sin a watan Maris.

Taron na bana mai taken "Asiya da Fasifik mai juriya, injin na ci gaban duniya" zai mai da hankali ne a kan batutuwan da suka shafi samun ci gaba mai dorewa bisa daidaito, inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin, da kuma cimma muradun Bogor, wato muradun da aka tsara cimmawa a garin Bogor na Indonesiya a shekara ta 1994, wanda aka tsara samar da hanyoyin kasuwanci da zuba jari a bayyane kuma ba tare da wani sharadi ba a yankin Asiya da Fasifik.

Wannan taron dai na yini biyu ya zo ne lokacin da ake fuskantar tangal tangal na ci gaban tattalin arzikin duniya, bukatar bada kariya ga ciniki da zuba jari, tsaikon da tattaunawar Doha na kasuwanci duniya ya samu, da kuma kokarin wajen kara azama ga tattalin arzikin kasashen yankin na Asiya da Fasifik.

A ganin jami'an diflomasiyya na Sin, ana sa ran Shugaba Xi zai kara bayyana matsayin kasarsa a kan batutuwa da suka hada da yanayin tattalin arzikin duniya a yanzu, matsayin kungiyar APEC wajen fidda tsarin hadin gwiwwa na kasuwancin tsakanin kasashen yankin, da kuma ci gaba mai dorewa na tattalin arziki cikin daidaito.

Tun da farko a ranar Litinin din sai da Shugaba Xi ya halarci taron tattaunawa da wakilan masu ba da shawara na 'yan kasuwan kungiyar APEC din tare da musayar ra'ayi a kan batutuwan da suka fi jawo hankali da suka hada da yanayin tattalin arziki na yankin Asiya da Fasifik. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v An fara taron APEC a Bali, kasar Indonesia 2013-10-06 16:36:28
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China