in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da a warware matsalar 'yan gudun hijira a Afirka
2014-10-06 18:40:59 cri

Daga ranar 29 ga watan jiya zuwa ranar Jumma'a 3 ga watan Oktoba, kwamitin zartaswa na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ya gudanar da taronsa karo na 65 a birnin Geneva, inda ya shirya taron musamman tsakanin manyan jami'ai kan matsalar 'yan gudun hijira a nahiyar Afirka. Mahalarta taron sun nuna damuwa sosai kan matsalar, tare da yin kira da a warware matsalar ta kyawawan hanyoyi daban daban.

A yayin taron, Wu Hailong, zaunannen wakilin kasar Sin da ke ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland ya nuna cewa, matsalar 'yan gudun hijira ta dora ma kasashen Afirka babban nauyi ta fuskar raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, tare da kawo illa ga zaman lafiyar da kwanciyar hankali a nahiyar. Ya kara da cewa, kasar Sin ta gabatar da ra'ayoyi hudu dangane da yadda ake tinkarar matsalar, na farko, ya kamata a kara zuba kudi kan warware matsalar, a zuba isasshen kudi cikin lokaci. Na biyu, wajibi ne a taimakawa juna wajen kara agazawa 'yan gudun hijira yadda ya kamata. Na uku, kamata ya yi a nuna tsaka-tsakanci da bin ka'idar jin kai bisa yadda abubuwa suka kasance, a kokarin hana sanya siyasa cikin matsalar 'yan gudun hijira. Na hudu, a tsaya tsayin daka kan warware rikici cikin ruwan sanyi, a mai da hankali kan barkewar rikici, a kokarin kawar da ainihin dalilin da ya sa mutane su tsere daga gidajensu.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China