in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNEP tace zuba jari a bangaren sauyin yanayi zai ingiza cigaban Afrika
2014-08-13 10:28:36 cri
An bukaci kasashen Afrika dasu mai da hankali wajen zuba jari a kananan ayyukan tinkarar sauyin yanayi domin habaka cigaban su, inji rahoton da ofishin ayyukan kula da muhalli ta MDD(UNEP)ta gabatar a ranar Talatan nan.

A cikin rahoton, an jaddada cewa zuba jari a bangaren yanayi zai inganta yankunan kasashen Afrika dake fama da gurbacewar muhalli, kiwon lafiya da kalubalen tattalin arziki.

Babban Directan Ofishin Achin Steiner ya bayyana cewa idan aka shigar da ayyukan tinkarar sauyin yanayi cikin manufar kasa ta samun cigaba,gwamnatoci za su samar da hanyoyi na samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, sannan a kare rayukan wassu miliyoyin al'umma.

Wani shirin na sa ido a kan ayyukan da za'a mai da hankali a kai a Afrika KTAA ya fitar da rahoton cewa ayyukan tinkarar sauyin yanayi zai fitar da hanyoyi da dama na amfanar tattalin arziki.

Kamar yadda Mr. Steiner ya lura, tattalin arzikin na Afrikan za su samu koma baya kwarai saboda sauyin yanayi idan har ba'a samar da wani mafita mai karfi ba.

Wannan rahoto har ila yau ya lura cewa cigaban tattalin arzikin Afrika zai samu koma baya saboda sauyin yanayi na kwatsam, don haka kamata yayi kasashen Afrika su bi tsarin da zai basu kwarin gwiwa wajen bin shirin kananan ayyukan sauyin yanayi don kare al'umma daga tsananin sauyin yanayin da za su iya fuskanta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China