in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yi kira ga kasashen Afirka da su gaggauta kyautata tsarin aikin gona
2014-06-24 14:49:31 cri
Sakataren gudanarwa na kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD Carlos Lopes, ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Afirka su gaggauta kyautata tsarin aikin gona, da yin kwaskwarima don sa kaimi ga samun bunkasuwa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba.

Mr Carlos ya bayyana hakan ne a gun taron kwamitin gudanarwa na kungiyar AU da aka gudanar a birnin Malabo. A cewarsa bunkasuwar aikin gona a kasashen Afirka a wadannan shekaru na yin tafiyar hawainiya, inda yawan kudin shiga da manoma suke samu ya ragu, don haka akwai bukatar gudanar da gyare-gyare ga manufofin aikin gona na kasashen dake nahiyar.

Carlos ya kara da cewa, idan aka kwatanta da shekaru 90 na karnin da ya gabata, za a ga yawan amfanin gona da aka samu a kasashen Afirka ya karu da kashin da bai haura 38 cikin dari kacal ba, koda yake wannan adadi ya karu da kaso 133 a kasar Sin.

Haka zalika Mr. Carlos ya ce, kamata ya yi kasashen Afirka su kara yin amfani da fasahar injiyoyi, da na kasuwanni wajen inganta aikin gona, tare da daga yawan kudin shiga da manoma ke samu.

Ya ce, bunkasar aikin gona zai daga darajar amfanin gona, kana zai taimakawa matasa wajen samun aiyukan yi. Ban da wannan, Carlos ya ce, domin samun nasarar kyautatuwar tsarin aikin gona a kasashen Afirka, ana bukatar kiyaye bunkasuwar tattalin arziki da zaman lafiya a kasashen nahiyar, tare da inganta fasahohin aikin gona, da samun iznin shiga kasuwanni, da kuma kara inganta masana'atu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China